Miyagun ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da babban jigon PDP yana hanyar zuwa kewayen gona
- Ana zargin ‘Yan bindiga sun tare motar Owere Dickson Imasogie a Uhunmwonde
- Dickson Imasogie da wasu mutum biyu sun hannun masu garkuwa da mutanen
- An dauke jagoran jam’iyyar na PDP ne yana kan hanyar zuwa gona a yau da safe
Edo - Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa wasu ‘yan bindiga sun dauke Dickson Imasogie, daya daga cikin kusoshin jam’iyyar PDP a jihar Edo.
Owere Dickson Imasogie ‘dan a mutun jam’iyyar PDP ne a jihar Edo, kuma babban manomi ne.
‘Dan siyasar yana da gonaki da dama a kudancin jihar Edo, rahotanni sun ce an dauke shi ne a lokacin da yake hanyar zuwa duba gonakin na sa.
An dauke wannan Bawan Allah ne a safiyar ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, 2021 a kan hanyar Agbor, yana shiirin zuwa wata gona a Uvbe.
Haka zalika jaridar Aminiya tace ‘yan bindigan sun hada da Direban Dickson Imasogie da wani mutum da ke cikin motar a lokacin da abin ya faru.
'Yan Sanda ba su da labari
Da aka tuntubi kakakin ’yan sanda na Jihar Edo, Bello Kongtons, domin jin abin ya faru, jami’in tsaron ya bayyana cewa bai da masiniya kan lamarin.
A wani kaulin da PM News ta fitar, an tare motar Owere Dickson Imasogie ne a yankin Obada da ke karkashin karamar hukumar Uhunmwonde, Edo.
Sun fada hannun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane da kimanin karfe 7:00 na safe. Har yanzu ‘yan bindigan dai ba su tuntubi iyalansu ba.
Edo State Decide Movement ta tabbatar da labarin
Tuni kungiyar Edo State Decide Movement ta fiar da jawabi, tana kira ga Mai girma gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya ceto wannan dattijo.
“Mun samu labari an yi garkuwa da ubanmu, abin koyinmu, mutum mai kyauta, Cif Dickson Imasogie da wasu mutane a kan titin Benin-Agbor.”
Edo State Decide Movement ta roki gwamna Obaseki ya kubutar da jigon na PDP da mutanensa.
Ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya fara yi wa majalisar FEC garambawul. Ocherome Nnanna yace akwai wasu Ministocin da ya kamata a fattake su.
Kamar yadda ku ka ji labari, a cikin jerin akwai Ministan tsaro, Janar Bashir Magashi. Marubucin yace da so samu ne a kori tsohon sojan daga matsayinsa.
Asali: Legit.ng