Biloniya zai gina sabon birni a hamada da N164trn, zai samar wa mutum miliyan 5 mazauni

Biloniya zai gina sabon birni a hamada da N164trn, zai samar wa mutum miliyan 5 mazauni

  • Biloniyan nan na Amurka, Marc Lore ya bayyana shirin sa na gina sabon birni a wata hamada da ke arewacin Amurka
  • Bisa kididdigar da ya yi, a kalla sai ya kashe dala biliyan 400 don samar da wuraren ayyuka, makarantu da sauran su
  • A cewar sa, birnin zai samar da gidaje ga mutane miliyan 5, kuma gine-ginen za su kasance masu kayatarwa kwarai

Amurka - Biloniyan Amurka mai suna Marc Lore ya bayyana shirye-shiryen sa na gina sabon birni a arewacin kasar.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar ya na shirin gina gidaje, wuraren ayyuka, makarantu da sauran su wadanda a kalla mutum zai isa ko wanne cikin mintuna 15.

Biloniya zai gina sabon birni a hamada da N164trn, zai samar wa mutum miliyan 5 mazauni
Biloniya zai gina birnin Telosa a Amurka. Hoto daga edition.cnn.com
Asali: UGC

Kamar yadda CNN ta ruwaito, sunan shirin Telosa kuma ya na shirin kashe dala biliyan 400 daidai da N164,400,000,000,000 don samar wa da mutane miliyan 5 wuraren rayuwa.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

A cewar sa, za a fara gina hamadar ne cikin salon gine-gine masu kayatarwa, za a samar da wutar lantarki da kuma ingantaccen ruwan sha da kayan masarufi.

Bisa tsarin, Telosa za ta yi amfani da 150,000 acres na fili don tallafa wa mutane miliyan 5 kuma za a yi amfani da shekaru 40 ne don kammala gine-ginen.

Za a yi amfani da shekaru 10 zuwa 20 wurin kammala tsari na farko sannan mutane miliyan 1 za su amfana.

Kamar yadda New York post ta wallafa, tun watan Yuni Lore ya nemo wani kamfani na Copenhagen mai suna Bjarke Ingels ya tsara gine-ginen birnin.

Biloniya zai gina sabon birni a hamada da N164trn, zai samar wa mutum miliyan 5 mazauni
Biloniya zai gina sabon birni a hamada da N164trn, zai samar wa mutum miliyan 5 mazauni. Hoto daga edition.cnn.com
Asali: UGC

Mazauna Telosa za su iya isa wuraren ayyukan su, makarantu ad sauran su cikin mintuna 15.

Babu wani tsayayyen wuri don tabbatar da shirin bangaren Nevada, Utah, Idaho, Arizona, Texas da Appalachian a birnin.

Kara karanta wannan

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

Jama'a sun yi martani

Nan da nan mutane suka fara tsokaci iri-iri a kafafen sada zumuntar zamani inda wani Jorene Soto ya ce:

“Me zai sa a gina katon birni irin wannan yayin da wasu wuraren suke fama da rashin ruwa mai kyau?

Wata Debbie Hesse ta ce:

“Wani garin na mutane miliyan 5 a cikin hamada— wurin da babu ruwa—-babbar magana.”

Wani Allan Robinson ya ce:

“Ya za a yi a yi gini a wuraren da babu ruwa?”

Obaseki: Babban tashin hankali na bayan na bar kujerar gwamna

A wani labari na daban, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a ranar Lahadi ya yi magana kan babban tashin hankalinsa da tsoro bayan ya bar kujerar gwamna.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, gwamnan da zai kammala mulkinsa karo na biyu a 2024, ya ce babban kalubalensa shi ne abinda zai faru da gyare-gyarensa nan da shekaru uku masu zuwa.

Kara karanta wannan

Obaseki: Babban tashin hankali na bayan na bar kujerar gwamna

Ya sanar da hakan ne a Benin, babban birnin jihar Edo yayin addu'ar ciki shekaru 87 ta Chief Gabriel Igbinedion da aka shirya a coci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel