Da Ɗuminsa: Hotunan mummunan ɓarnar da ambaliyar ruwar da ta halaka mutane 3 a Abuja ta yi
- Ambaliyar ruwa ta yi barna a rukunin gidajen Trademore a Lugbe babban birnin tarayya Abuja
- Mazauna unguwar sun ce ambaliyar ruwar ya fara ne a ranar Litinin bayan ruwan sama mai karfi da aka yi
- Kawo yanzu an gano gawarwakin mutane uku sannan ruwan ta lalata motocci da kayayyakin al'umma da dama
FCT, Abuja - A kalla gawarwakin mutane uku ne aka gano a safiyar ranar Litinin a rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe, babban birnin tarayya, Abuja, Premium Times ta ruwaito.
Rahoton na Premimum Times ya ce mazauna unguwar sun ce ambaliyar ruwan ya fara ne a safiyar ranar Litinin bayan ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Ambaliyar ruwar ya yi sanadin bacin motocci da wasu kayayyakin mutane da dama a unguwar.
Jami'an hukumar kwana-kwana na birnin tarayya Abuja sun isa wurin a safiyar ranar Litinin domin kai wa mutane dauki.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
A kan samu irin wannan ambaliyar ruwar a unguwar a duk damina na kowanne shekara.
Ku saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng