Gwamna har ya hango Jam’iyyar APC ta samu nasara da kuri’u miliyan 30 a zaben 2023

Gwamna har ya hango Jam’iyyar APC ta samu nasara da kuri’u miliyan 30 a zaben 2023

  • Aminu Bello Masari yana ganin lokaci kawai ake jira a ji APC ta lashe zaben 2023
  • Gwamnan Katsina ya bugi kirji, yace jam’iyyar APC za ta yi nasara a zaben mai zuwa
  • Masari ya fadi wannan ne ganin APC ta shirya zabuka hankali kwance a Katsina

Katsina - A ranar Laraba, 8 ga watan Satumba, 2021, gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta ci zabe ta gama a 2023.

Punch tace gwamnan ya yi wannan jawabi ne da daddare, ganin irin nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a zabukan mazabu da na kananan hukumomi.

Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya samu kwarin gwiwa da adadin mabiyan da jam’iyyar APC mai mulki ta ke da su kamar yadda rajistanta yake nuna wa.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Masari ya yaba da aikin da APC ta yi

Aminu Masari ya na mai wannan sa rai ne a lokacin da ya karbi rahoton zaben shugabannin kananan hukumomi na APC da Aliyu Kumo ya gabatar.

“Jam’iyyar APC tayi kokari ko ina a fadin kasar nan. Za mu koma mu gudanar da zaben shugabannin na jihohi, sai ayi zabe na kasa, inda za a fitar da shugabannin jam’iyya.”

Jam’iyyar APC
Buhari yana kamfe a Katsina Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Yadda za mu samu kuri'a akalla miliyan 30 - Masari

This Day ta rahoto Masari yace ko da 70% na ‘ya ‘yan APC da suka yi rajista ne za su kada kuri’a a 2023, za su tashi da kuri’u miliyan 30 a zaben shugaban kasa.

A cewar Gwamnan na Katsina, lokaci kurum ake jira, a tabbatar da jam’iyyar APC ta koma mulki. Sannan ya bayyana yadda APC ta bi, ta fito da shugabanninta.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana wanda ya dace da mulki, ya cire Osinbajo, Tinubu a lissafin 2023

“Saboda haka za mu iya cewa muna daf da kai ga nasara. Za mu kai lokacin, kuma za mu kai ga ci.”

Gwamna Masari yace sababbin shugabannin APC na kananan hukumomi 34 da gundumomi 361 sun fito ne ta hanyar yi masu mubaya’a da aka yi a fadin jihar.

Da yake bayani, shugaban gudanar da zaben na APC, Aliyu Kumo, ya yaba da yadda aka gudanar da zaben, yace babu wasu ‘yan taware da suka kawo matsala.

Sanata Wammako da Abdulaziz Yari sun je Landan

A ranar Laraba ne aka i cewa Sanata Aliyu Magatakarda Wammako da Abdulaziz Yari sun kai wa Asiwaju Bola Tinubu ziyara yayin da aka ce yana jinya a ketare.

'Yan siyasar sun dauki hotuna, kuma wannan ne karo na farko da Tinubu ya dauki hoto ba tare da an ga ya dogara sanda ba, hakan yasa ake tunani ya samu sauki.

Kara karanta wannan

Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri

Asali: Legit.ng

Online view pixel