Aisha Buhari ta caccaki Dr Pantami, ta ce ya cire tsoron kowa ya yi abinda ya dace

Aisha Buhari ta caccaki Dr Pantami, ta ce ya cire tsoron kowa ya yi abinda ya dace

  • Uwar gidan shugaba kasa, Aisha Buhari ta caccaki ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami
  • Ta bukaci ya ji tsoron Allah ya yi abinda ya dace wa 'yan kasa yayin da ta yada wani bidiyo nasa
  • Ta lika bidiyon malamin kuma minista tare da cewa: 'A chire tsoro a yi abinda ya dace' a shafinta na Instagram

Uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari a ranar Lahadi 12 ga watan Satumba ta yada wani bidiyon da ke nuna Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami, yana kuka yayin daya daga cikin wa’azinsa na baya-bayan nan.

Pantami ya kasance mai yawan kuka yayin zaman tafsirinsa lokacin da ake karanta wasu ayoyi a cikin Alƙur'ani Mai Girma, ko lokacin da yake bayanin musgunawa Musulmi.

Aisha Buhari ta yada bidiyon a shafinta na Instagram tare da wata sanarwa mai tsauri: “A chire tsoro a yi abinda ya dace”.

Kara karanta wannan

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

Aisha Buhari ta caccaki Dr Pantami, ta ce ya ji tsoron Allah ya yi abinda ya dace
Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cikin gajeren bidiyon, Pantami da mai ja masa baki sun fashe da kuka lokacin da ministan ya nemi mai karatun ya karanta wata aya akan tsoron Allah.

Alaramma mai jan baki ya jawo aya ta 63 ta Suratu Maryam, ayar da ke magana kan sakamakon da Allah zai yi wa bayinsa masu tsoron Allah.

Yayin da Pantami ya fara sharhin ayar, shi ma ya fashe da kuka, yana cewa:

“Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu. Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu. Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu.”

Aisha Buhari ta saba da sukar mijinta da mukarrabansa

Uwargidan shugaban kasa ta shahara wajen sukar gwamnatin mijinta da wasu masu nade-naden gwamnatinsa.

Ba sau daya ba, an sha samun maganganu da dama na Aisha Buhari inda take sukar gwamnatin Buhari da wasu mukarrabansa.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

A wata hira da BBC a 2016, Aisha Buhari ta bayyana yadda wasu kalilan din mutane suka zagaye shuga Buhari, kuma su kadai suke amfana.

A cewarta, shugaban bai san yawancin jami’an da ya ke nadawa ba.

Kalli bidiyon:

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

A wani labarin, Babban limamin masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters dake Abuja, Sheikh Muhammad Khalid, kwanan nan ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon wa’azin sa da ya soki shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bazu.

A cikin wata hirar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Punch, malamin addinin Islaman ya ce yana tsaye kan kalamansa cewa shugaban bai tsinana komai ba.

A tattaunawar, malamin ya bayyana abubuwan da suke damunsa game da gwamnatin shugaba Buhari, wadanda a cewarsa gwamnatin ta cika yiwa 'yan Najeriya karerayi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Wuta ‘yan bindiga za su, fadar Shugaban kasa ta mayar da martani ga Sheikh Gumi

Asali: Legit.ng

Online view pixel