Jajiberin zuwan Buhari Imo: Gwamnatin jiha ta ja kunnen 'yan IPOB da kakkausar murya

Jajiberin zuwan Buhari Imo: Gwamnatin jiha ta ja kunnen 'yan IPOB da kakkausar murya

  • Gwamnatin jihar Imo ta ja kunnen IPOB su kama kan su a ranar Alhamis lokacin da shugaba Muhammadu Buhari zai kawo ziyara
  • Shugaban kasar zai kaddamar da wasu ayyuka ne na gwamnan jihar Imo, Gwamna Hope Uzodinma a ranar Alhamis
  • An samu rahotanni a kan yadda IPOB ta bai wa jami’anta umarnin zama a gida, sun ce basu bukatar Buhari a wani yankin kudu maso gabas

Imo - Gwamnatin jihar Imo ta ja kunnen 'yan IPOB a kan su tsaya a mazauninsu yayin kai ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ana sa ran a ranar Alhamis shugaban kasan zai kaddamar da wasu ayyukan Gwamna Hope Uzodinma.

Jajiberin zuwa Buhari Imo: Gwamnatin jiha ta ja kunnen 'yan IPOB da kakkausar murya
'Yan tawayen IPOB yayin da suke tattaki dauke da tutocinsu. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

An samu rahotanni a kan yadda IPOB ta bai wa mutanen ta umarnin zama a gida a ranar Alhamis, inda suke cewa ba su bukatar shugaban kasa a wani bangare na kudu maso gabas, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari a Imo: Inyamurai sun ce za su fito kwansu da kwarkwata su tarbi Buhari

Sai dai kwamishinan labarai na jihar, Declan Emelumba, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Owerri ranar Laraba, ya ja kunnen mutanen jihar inda yace wajibi ne a amshi shugaban kasar da hannaye biyu.

A cewar sa:

“Ban ji labarin wata kungiya ta bayar da umarnin zaman gida ba. Wanda na ji shi ne na masu zanga-zangar neman a sakin musu shugaban su duk ranar da ya bayyana a kotu.”
“Amma wannan batun shugaban kasa ya kawo ziyara ake yi. Wannan kuwa ziyara ce shugaban kasa zai kawo jihar Imo kuma za mu yi iyakar kokarin mu na ganin mun sauke shi da kyau.
"Mun shirya duk wasu jami’an tsaro don kariya a gare shi kuma ina mai tabbatar muku jami’an Imo suna maraba da shi.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Imo na shirin tarbar shugaba Buhari, inji kwamishina

Emelumba ya bayyana ziyarar shugaban kasar a matsayin ziyara ta musamman kuma karo na farko da zai kawo ziyara jihar da kan shi.

Kwamishinan ya ce, mazauna jihar suna Allah-Allah su amshi shugaban kasar, don haka ne ma ‘yan kasuwan su za su rufe kasuwa a ranar Alhamis.

A cewar sa, shugaban zai kaddamar da ayyuka 4, cikin su akwai titin Ihiagwa zuwa Nekede, Fasahar Balloon wacce aka yi gada ta karkashin kasa ta bullo ta saman titin Chukwuma Nwoha, titin Naze/Nekede/Ihiagwa, Egbeda By-Pass da sauran su.

Taliban ta sanar da sabon shugaba da sabbin ministoci

A wani labari na daban, kungiyar Taliban ta sanar da Mullah Mohammed Hassan Akhund a matsayin sabon shugaban gwamnatinta a Afghanistan a yau Talata, The Punch ta ruwaito.

Babban mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid ya shaidawa manema labarai ya sanar da cewa wanda aka kafa Taliban da shi Abdul Ghani Baradar shine zai zama mataimakin shugaban kungiyar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

Sauran nade-naden sun hada da Mullah Yaqoob a matsayin ministan tsaro na riko, Amir Khan Muttaqi a matsayin ministan riko na harkokin kasashen waje sai Mullah Abdul Ghani Baradar and Mullah Abdul Salam Hanafi a matsayin mataimakansa biyu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel