Alƙali ya bada umurnin a bawa lebura masauki a gidan ɗan kande kan satar masara na N63,000 a wata gona

Alƙali ya bada umurnin a bawa lebura masauki a gidan ɗan kande kan satar masara na N63,000 a wata gona

  • Kotu ta bada umurnin a ajiye mata wani lebura mai suna James Joseph a gidan gyaran hali
  • Alkalin kotun A.A. Ayeni ya bada wannan umurnin ne bayan wanda ake zargin ya amsa tuhumarsa na satar masara daga gonar wani
  • Dan sanda mai gabatar da kara, Emmanuel Abdullahi ya shaidawa kotu Joseph ya sace masara da kudinsa ya kai N63,000

Osun - Wata kotun majistare da ke zamanta a Ile-Ife a jihar Osun, a ranar Alhamis, ta bada umurnin a ajiye mata wani lebura, James Joseph, mai shekaru 30 a gidan gyaran hali.

The Punch ta ruwaito cewa kotun ta bada wannan umurnin ne bayan wanda ake zargin ya amsa laifin satar masara a wata gona.

Alƙali ya bada umurnin a bawa lebura masauki a gidan ɗan kande kan satar masara na N63,000 a wata gona
Kotu ta bada umurnin a bawa lebura masauki a gidan ɗan kande kan satar masara na N63,000 a wata gona. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Rundunar yan sanda ne ta gurfanar da Joseph kan zargin sata.

Alkalin, A.A. Ayeni ya bada umurnin a ajiye Joseph a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci.

Acewar rahoton na The Punch, Ayeni ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 23 ga watan Satumba kafin yanke hukunci.

Tunda farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Emmanuel Abdullahi ya shaidawa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Satumban 2021 a kauyen Ogudu a Ile-Ife.

Abdullahi ya ce wanda ake zargin ya sace masara da kudinsa ya kai N63,000 mallakar Olarewaju Johnson.

Ya ce wanda ake zargin ya aikata abin da zai iya tada zaune tsaye a lokacin da ya kutsa gonar Johnson.

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.

A cewar rahoton na LIB, Bayan samun rahoton ne kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya umarci jami’an sa wanda ya sa SP Shehu ya jagorance su kamo wanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel