Da dumi: Soji sun damke babban dan Boko Haram, sun kama buhuhunan sinadaran hada Bam 281
- Dakarun Sojin Najeriya sun samu nasarar damke masu kaiwa Boko Haram sinadaren hada Bam
- Sojin rundunar Operation Hadin Kai sun damke dan Boko Haram da aka dade ana nema
- An kama buhuhunan sinadarin Urea kimamin 300 da ake amfani wajen hada Bam
Abuja - Hukumar Sojin Najeriya ta samu nasarar damke kasurgumin dan Boko Haram a Arewa maso gabas kuma ta kai simame ma'ajiyar sinadaran hada bama-bamai a Borno da Yobe.
Diraktan hulda da jama'a na hukumar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a jawabin da ya saki a shafin Facebook.
Yace wannan nasara ya biyo bayan hare-haren da rundunar Operation HADIN KAI (OPHK) suka kai.
Yace:
"Dakarun Sector 2 Joint Task Force na Operation HADIN KAI (OPHK) sun damke wani babban dan Boko Haram kuma sun kai simame ma'ajiyar ajiyan sinadaran hada bama-bamai a Damboa dake jihar Borno; da kuma Gashua dake jihar Yobe."
"Sakamakon cinne, an damke wani dan ta'addan BH/ISWAP da aka dade ana nema ruwa a jallo a hanyar Damboa-Wajiroko."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa Sojoji sun kwato buhuhunan sinadarin Urea 281 a ma'ajiyoyi daban-daban kuma an damke masu kaiwa Boko Haram wadannan kayayyaki mutum biyu.
Yace:
"Hakazalika, Sojoji sun samu nasarar damke wasu masu kaiwa yan ta'adda sinadaran hada bama-bamai. Kasuwar ta shahara da taya yan Boko Haram boye sinadaren."
"A harin da aka kai, an damke buhuhunan Urea 281 daga kasuwar kuma an damke masu sayarwa Boko Haram."
Kimanin yan Boko Haram 6000 suka mika wuya kawo yanzu
A bangare guda, hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana adadin yan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya ga hukuma a yankin Arewa maso gabas cikin makonni uku da suka gabata.
Dirkatan yada labaran hedkwatan, Birgediya Janar Benard Onyeuko, a jawabin da ya saki ranar Alhamis ya bayyana cewa yan ta'adda 5,890 tare da kwamandojinsu suka mika wuya kawo yanzu ga jami'an Sojojin Najeriya.
Asali: Legit.ng