Da duminsa: Kimanin yan Boko Haram 6000 suka mika wuya kawo yanzu

Da duminsa: Kimanin yan Boko Haram 6000 suka mika wuya kawo yanzu

  • Hedkwatar tsaro ta ce kimanin yan Boko Haram 6000 sun mika wuya cikin yan makonni
  • Daga cikinsu akwai kwamandoji tare da matansu da yaransu
  • Duk da haka Sojojin sun ragargaji wasu yan ta'addan ISWAP ranar Laraba

Abuja - Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana adadin yan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya ga hukuma a yankin Arewa maso gabas cikin makonni uku da suka gabata.

Dirkatan yada labaran hedkwatan, Birgediya Janar Benard Onyeuko, a jawabin da ya saki ranar Alhamis ya bayyana cewa yan ta'adda 5,890 tare da kwamandojinsu suka mika wuya kawo yanzu ga jami'an Sojojin Najeriya.

Bernad Inyeuko yace:

"A sani cewa cikin yan makonnin a suka gabata, sama da yan ta'adda 5,890 wanda ya hada da kwamandoji da mabiyansu da iyalansu sun mika wuya ga Sojoji a yankin Arewa maso gabas."

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a Borno, sun kashe 6

"An mika mutum 565 da suka hada da kwamandoji 3, Amirai 4, Nakibai 5, da barayin shanu 5 cikin wadanda suka mika wuya tare da iyalansu ga gwamnatin jihar Borno bayan bincike kansu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Kimanin yan Boko Haram 6000 suka mika wuya
Da duminsa: Kimanin yan Boko Haram 6000 suka mika wuya kawo yanzu Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Me yasa suke mika wuya?

Daya daga cikin wadanda suka mika wuya, Modi Malaram ya cewa yanzu haka akwai rabuwar kai tsakanin kwamandojin kuma haka ya sa suka iya fitowa mika wuya.

Yace:

"Bayan mutuwar Shekau, an samu sabanin cikin gida da fadace-fadace, kuma hakan ya faranta mana rai.

Amma kuma ruwan wutan da sojoji keyi ya tilasta mana guduwa daga sansaninsu. Haka yasa muka fito don mika wuya,"

"Wallahi, yawancinmu yara ne kuma marasa karfi na yakan kwamandojin Boko Haram da suka sacemu daga kauyukanmu."

"Tun a baya mun san kungiyar na shaidanu ne, amma mun kasa yaki da su saboda kashemu za'a yi. Wadanda sukayi kokarin guduwa a gabanmu aka kashesu."

Kara karanta wannan

Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyara Fadar Shehun Borno, Ya Yi Magana Kan Mayakan Boko Haram Dake Mika Wuya

Akwai rabuwar kai tsakanin kwamandojin Boko Haram

Wata majiyar daban ta bayyanawa PRNigeria cewa rabuwar kan dake tsakanin bangarorin biyu ya sake munana ne lokacin da aka kashe wasu yan ta'addan Boko Haram kan wasu laifukan da basu taka kara sun karya ba, da kuma kin basu mukamai manya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng