Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga 7 da suka kashe 'dan Sarkin Kontagora, Bashir Namaska

Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga 7 da suka kashe 'dan Sarkin Kontagora, Bashir Namaska

- Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka masu garkuwa da mutane 7

- Tsagerun yan bindigan ne suka kai hari gonar Sarkin Kontagora

- An yi rashin Sardaunan Kontagora sakamakon harin

Gamayyar jami'an hukumar Sojojin Najeriya da na yan sanda a karamar hukumar Kontagora sun ragargaji yan bindiga akalla guda bakwai a cikin daji a jihar Neja.

PRNigeria ta tattaro cewa kwamandan 311 Artillery, T.O Olukukun, da kwamandan yan sandan, Haruna Adamu Swapo ne suka jagoranci farkamin da aka kaiwa yan bindigan.

Yan bindigan na guduwa nee bayan harin da suka kai gonar Sarkin Kontagora a kauyen Masuga kuma suka hallaka 'dansa, Sardaunan Kontagora, Alhaji Bashir Namaska.

Jami'an tsaron sun kure musu gudu cikin daji kuma suka hallakasu.

Sauran kuwa sun gudu da raunukan harbi.

Daya daga cikin yan bindigan da aka kama wanda ya mutu daga baya ya gaza magana da Turanci ko Hausa, yaren Fulfulde kawai yayi.

Yan bindigan da suka kai hari gonar sarkin sun shiga ne ta daji mallakin hukumar Sojojin Najeriya.

KU KARANTA: Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru

Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga 7 da suka kashe 'dan Sarkin Kontagora, Bashir Namaska
Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga 7 da suka kashe 'dan Sarkin Kontagora, Bashir Namaska Hoto: Fulani
Asali: Facebook

KU KARANTA: Akalla sau 6 ya zo Borno, ya lashi takobin kawar da Boko Haram: Zulum ya yi jimamin rashin Attahiru

Mun kawo muku rahoton cewa Dan gidan Sarkin Kontagora, Alhaji Bashar Saidu Namaska, na cikin mutanen da yan bindiga suka hallaka yayinda suka kai hari gonar Sarkin a ranar Laraba, 19 ga Mayu, 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'dan Sarkin na tare da wasu mutane ne cikin gona dake titin Zuru lokacin da yan bindiga suka kai musu farmaki.

Yan bindigan sun yi awon gaba da shanu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel