Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Owerri, jihar Imo

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Owerri, jihar Imo

Labarin dake shigowa da duminsa na nuna shugaba Muhammadu Buhari ya dira Owerri, babbar birnin jihar Imo da safiyar Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021.

Buhari ya amsa gayyatar da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, yayi masa domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatinsa ta kammala.

Kwamishinan yada labarai na Imo, Declan Emelumba, ya ce gwamnatin jihar na shirin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa an shirya shugaban kasar zai kai ziyarar aiki zuwa Imo don kaddamar da wasu ayyukan da jihar ta aiwatar.

Ziyarar Shugaban a Imo ita ce ziyarar aiki ta farko a jihar tun hawan sa mulki a shekarar 2015 kuma a karon farko jihar za ta karbi bakuncin Shugaban kasa a ziyarar aiki tun 2009.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Owerri, jihar Imo
Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Owerri, jihar Imo
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutan jihar sun ce za su fito kwansu da kwarkwata su tarbi Buhari

Matasan kabilar Igbo sun sha alwashin taruwa domin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Imo, a ranar Alhamis, lokacin da zai ziyarci jihar don kaddamar da ayyukan gwamnan jihar, Sanata Hope Uzodinma.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Onwuasoanya Jones Mataimakin Shugaban kungiyar matasan Igbo ta Ohanaeze Ndigbo Worldwide.

Onwuasoanya ya yi gargadin cewa duk wanda ke kokarin cin zarafin wadanda ke son zuwa don maraba da Shugaban kasar zuwa jihar Imo za a dauke shi a matsayin masu son tada zaune tsaye ba wai wanda ke wakiltar maslahar Igbo ba.

Zuwan Buhari Imo: Gwamnatin jiha ta ja kunnen 'yan IPOB da kakkausar murya

Kara karanta wannan

Jajiberin zuwan Buhari Imo: Gwamnatin jiha ta ja kunnen 'yan IPOB da kakkausar murya

Gwamnatin jihar Imo ta ja kunnen 'yan IPOB a kan su tsaya a mazauninsu yayin kai ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

An samu rahotanni a kan yadda IPOB ta bai wa mutanen ta umarnin zama a gida a ranar Alhamis, inda suke cewa ba su bukatar shugaban kasa a wani bangare na kudu maso gabas, Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai kwamishinan labarai na jihar, Declan Emelumba, a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Owerri ranar Laraba, ya ja kunnen mutanen jihar inda yace wajibi ne a amshi shugaban kasar da hannaye biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel