Zaben Shugabanni ya jawo rikicin gida yana neman ya kacame a Jam’iyyar APC a Legas
- Neman shugabanci ya raba kan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a garin Ifako/Ijaye
- Da farko ‘yan APC suna tare da Kofoworola Ajayi, yanzu lissafin ya canza
- Ana rade-radin masu ruwa da tsaki sun dawo goyon-bayan Deacon Omole
Lagos - Rahotanni daga jaridar Punch sun bayyana cewa ana fama da rikicin gida a jam’iyyar APC a yankin karamar hukumar Ifako/Ijaye a jihar Legas
An samu sabani tsakanin mabiya jam’iyyar ta APC ne a sakamakon zaben shugabannin kananan hukumomi da aka gudanar a makon da ya gabata.
Jaridar tace hanyar da za a bi wajen tsaida shugabannin jam’iyyar APC a matakin kananan hukumomi ne ya raba kan wasu daga cikin ‘yan APC.
An yi wa Kofoworola Ajayi mubaya'a
Wata takarda da ta shiga hannun ‘yan jarida ta nuna masu ta-cewa sun tsaida Kofoworola Ajayi a matsayin wanda za ta zama shugabar APC a Ifako/Ijaye.
Shugabannin APC da jagororin jam’iyyar mai mulki a Ifako/Ijaye sun amince da Kofoworola Ajayi. Amma abubuwa suna neman canza zani a halin yanzu.
Daga cikin wadanda suka yi mata mubaya’a akwai; Otunba Yomi Ogunnusi; Nurudeen Akinwunmi, Toba Oke, Dayo Fafunmi, da Akin Fadayomi.
Sai Salvador Adebayo, Rotimi Adeleye, Temitope Adewale, Demola Doherty, Usman Hamzat, Seni Tobun, Kunle Olayinka, Rajh-Label, da kuma Banjo Omole.
Lissafi yana neman ya canza
Daga baya sai aka ji ana cewa irinsu Temitope Adewale sun ziyarci Bola Tinubu a Landan, inda aka canza yadda za a fito da shugabannin jam’iyyar APC.
“Bayan duk mun yarda da sunayen da aka fitar, wasu sun canza ra’ayi. Suna ikirarin Tinubu bai gamsu da matakin ba, suka kira shi a waya, suka kai kuka.”
“Muna kira ga Tinubu ya yi magana a kan murde zaben da ake shirin yi. Wannan ne abin da ya faru a lokacin zaben shugabannin kananan hukumomi.”
Majiyar tace bayan an tsaida magana daya a kan Ajayi, yanzu an fara neman yadda za a ba Deacon Omole wannan kujera, akasin yarjejeniyar da aka yi.
An gagara sulhu a PDP
A makon nan aka ji gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya kafe a kan bakarsa, ya rantse sai an fatattaki Uche Secondus daga kujerar shugaban jam'iyyar PDP.
Gwamnan ya na cikin wadanda suka dage sai Uche Secondus ya zama shugaban jam’iyya a shekarun da suka wuce, amma yau sabani ya shiga tsakaninsu.
Asali: Legit.ng