Gwamna El-Rufai ya yi magana game da rade-radin toshe layukan wayoyin kowa a jihar Kaduna
- Gwamnatin jihar Kaduna ta musanya rade-radin rufe hanyoyin sadarwa na waya
- Malam Nasir El-Rufai ya fitar da jawabi a ranar Talata, yace ayi fatali da labaran
- Gwamna El-Rufai yace idan akwai bukatar hakan, za a sanar da mutanen Kaduna
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta yi magana game da rade-radin da ake yi na cewa ana shirin toshe kafofin sadarwa, tace wannan ba gaskiya ba ne.
Mai girma gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai ya yi maza ya fitar da jawabi a ranar Talata, 7 ga watan Satumba, 2021, da rade-radin suka soma yawo.
Malam Nasiru El-Rufai ya fitar da jawabi na musamman ta bakin mai taimaka masa wajen yada labarai da sadarwa, Mista Muyiwa Adekeye a jiya da dare.
"Babu batun kashe layukan waya a jihar Kaduna"
A jawabin da ya yi wa take da “No telecoms shutdown in Kaduna State”, gwamna El-Rufai yace labarin bogi ne ke yawo, ya kuma yi kira ayi fatali da shi.
Punch ta wallafa labarin kamar yadda gwamnan ya bayyana a shafinsa na Facebook, yana cewa idan za a toshe hanyoyin sadarwa, za a sanar da al’umma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin da Gwamna ya fitar
“Gwamnatin Kaduna ba ta da shirin kashe kamfanonin sadarwa, ba ta dauki wannan mataki ba, kuma ba ta bada sanarwar wannan shiri ba.”
“Gwamnatin jihar Kaduna ba ta tuntubi wata hukumar tarayya, tana rokon a toshe layukan wayoyi ba, kuma ba ta bada umarni ayi hakan ba.”
“Mazaunan Kaduna suyi watsi da wannan jita-jita. Labaran bogi ne wasu ke yada wa a matsayin na gaske ta hanyar daura tambarin gwamnati.”
“A takaice dai duk wadannan ba gaskiya ba ne. Mazauna su yi fatali da wadannan labarai na bogi. Ba za a rufe layukan wayoyi a jihar Kaduna.”
“Gwamnatin Kaduna ba ta wani boye-boye a game da abin da ya shafi harkar tsaro. Idan akwai bukatar a toshe layuka, za a sanar da al’umma.”
NCC ta dakile hanyoyin sadarwa a Zamfara
A baya an ji gwamnatin tarayya ta bada umarnin a dakatar da ayyukan kamfanonin sadarwa a fadin jihar Zamfara domin a iya shawo kan matsalar tsaro.
Bayan datse layukan jama'a, rahotanni sun zo mana cewa jiragen yakin sojojin sama sun yi ta yin luguden wuta a duk sansanonin 'yan bindigan da ke jihar.
Asali: Legit.ng