Ya kamata a duba kwakwalwarka, kada Allah ya maimaita mana irin Buhari: Wike ga Umahi

Ya kamata a duba kwakwalwarka, kada Allah ya maimaita mana irin Buhari: Wike ga Umahi

  • Gwamnan Rivers ya yi martani mai zafi ga gwamnan Ebonyi kan addu'an da yayi
  • Umahi yayi addu'an cewa Allah ya maimaita mana Buhari a 2023
  • Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamna Umahi ranar Litinin

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a ranar Laraba ya caccaki takwararsa na jihar Ebonyi, Dave Umahi, wanda yace Allah ya ba Najeriya shugaba irin buhari a 2023.

Umahi a ranar Litinin yayinda ya kaiwa Buhari ziyara fadar shugaban kasa, yayi addu'an Allah ya maimaitawa Najeriya mutum mai kirki irin Buhari a 2023.

Amma ranar Laraba, Wike yayi raddi mai zafi ga Dave Umahi inda yace ko shugaba Buhari ya san Allah ba zai ba Najeriya shugaba irinsa a 2023 ba, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya sallami shugaban NAPTIP, Basheer Garba

Yace:

"Haka wani gwamna ke cewa yana addu'a Allah ya maimata mana irin Buhari."
"Sai nace wai me matsalar shi ne? Shin baku ganin akwai bukatar duba kwakwalwarsa? Jahilci kawai."
"Kuma ka san Shugaban kasa ya san karya kake masa. Shi (Buharin) ya sani. Abin dai akwai takaici. Allah ya iya mana."

Ya kamata a duba kwakwalwarka, kada Allah ya maimaita mana irin Buhari: Wike ga Umahi
Ya kamata a duba kwakwalwarka, kada Allah ya maimaita mana irin Buhari: Wike ga Umahi Hoto: Punch
Asali: Facebook

Wike ya yi Alla-wadai da irin rashin tsaron da Najeriya ke fuskanta karkashin Buhari da kuma rashin adalcin dake faruwa.

Gwamnan yayi maganan ne a taron masu ruwa da tsaki a birnin jihar Fatakwal inda yake jawabi ga yan kasuwa kan rikicin kudin harajin da yake da hukumar FIRS.

Wike da Umahi sun dade suna ja'inja tun lokacin da gwamnan na Ebonyi ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Kashi 55% na nade-naden da Buhari yayi yan kudancin Najeriya ya baiwa, Hadimin Shugaban kasa

Me Dave Umahi ya fadi?

Dave Umahi, ya bayyana fatan wanda ke da “kyakkyawar zuciya” kamar Shugaba Muhammadu Buhari zai fito a matsayin wanda zai maye gurbinsa a 2023.

Ya fadi hakan ne duk da cewar ya ce ya yi wuri sosai da za a shiga harkokin siyasar 2023 kamar yadda ya lura cewa hakan zai zama shagala a bangaren shugaban kasa da gwamnonin jihohi.

Ya kuma kara da cewa membobin jam’iyyun siyasa daban-daban daga Kudu maso Gabas suna aiki a cikin jam’iyyunsu don tabbatar da ganin cewa an mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel