Gwamnatin Filato ta kara sassauta dokar hana fita a Jos ta Arewa, tare da dage dokar hana adaidaita sahu
- Gwamnatin Filato ta janye dokar hana tuka Keke NAPEP a garin Jos da kewaye tare da sassauta dokar hana zirga-zirga, a Karamar Hukumar Jos ta Arewa
- Gwamnan Jihar, Simon Lalong, ne ya amince da hakan bayan kammala taron Majalisar Tsaron Jihar
- A yanzu dokar hana zirga-zirga ta dawo daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe
Filato - Gwamnatin jihar Filato ta sanar da sake sassauta dokar hana fita a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Dakta Makut Macham ya fitar, ya bayyana cewa gwamnati ta kuma dage haramcin da aka sanya a baya a kan tuka adaidaita sahu a jihar.
Macham ya bayyana cewa gwamnan ya amince da hakan ne a ranar Talata bayan taron kwamitin tsaro na jihar da aka gudanar a sabon gidan gwamnati a Jos, Aminiya ta ruwaito.
Sanarwar ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Daga ranar Laraba, 8 ga Satumba 2021, dokar hana fita a Jos ta Arewa za ta fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
“Wannan zai yi daidai da matsayin dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Kudu da Bassa wanda har yanzu yana daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
“Hakanan, Gwamna Lalong ya kuma amince da cewa daga ranar Laraba, 8 ga Satumba 2021, za a dage dokar hana zirga -zirgar adaidaita sahu daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a kullum. Wannan yana nufin cewa ba za a bar wani adaidaita ya yi aiki tsakanin awanni 6 na yamma zuwa 6 na safe ba.”
Sai dai gwamnan, ya bayyana cewa haramcin babura a cikin garin Jos/Bukuru zai ci gaba da aiki, yana mai cewa za a ci gaba da tabbatar da ganin an kama masu laifin da kuma hukunta su kamar yadda doka ta tanada.
Gwamnan ya yabawa al'umman jihar kan haɗin kai da fahimtar da suka nuna a lokacin hare-haren da kuma dokar hana fita.
Ya bukace su da su ci gaba da marawa gwamnati baya don dawo da zaman lafiya a fadin jihar, Channels TV ta ruwaito.
Kisan Jos: Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar cafke mutanen da ke da hannu a kashe-kashen da aka yi a jihar Filato.
A cikin watanni uku da suka gabata, hare-hare a sassa daban-daban na jihar sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari.
Buhari, wanda Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya wakilta, a wani zaman tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki a jihar a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, ya bukaci tattaunawa mai dorewa don samar da zaman lafiya a Filato.
Kwanaki bayan ganawa da Tinubu, shahararren gwamnan APC ya magantu akan kudirin takarar shugaban kasa
Asali: Legit.ng