Kogi ga EFCC: Zargin waskar da kudi da ku ke yi daidai yake da labaran 'A sha ruwan tsuntsaye'

Kogi ga EFCC: Zargin waskar da kudi da ku ke yi daidai yake da labaran 'A sha ruwan tsuntsaye'

  • Gwamnan jihar Kogi ya musanta zargin da EFCC ta ke yi mata na yasar dukiyar gwamnati da adana su a asusun banki don samun riba
  • Kwamishinan labaran jihar, Kingsley Fanwo ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis
  • Fanwo ya ce kamata yayi a ce EFCC ta na yaki da rashawa ba wai ta dinga kwakulo laifuka ta na danna wa wanda bai ji ba bai gani ba

Lokoja, Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta musanta zargin da hukumar EFCC ta ke yi mata na adana wasu kudaden albashi a asusun ta domin a samu riba.

Kamar jaridar TheCable ta wallafa, a watan da ya gabata babbar kotun jihar Legas ta daskarar da asusun albashin jihar kogi na wani banki a kan amsar bashin naira biliyan 20 daga bankin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta kori Gwamna Buni a matsayin shugaban riko na APC, ta dakatar da taron karamar hukuma

Kogi ga EFCC: Zargin waskar da kudi da ku ke yi daidai yake da labaran 'A sha ruwan tsuntsaye'
Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yayi wa EFCC wankin babban bargo kan zargin waskar da wasu kudade. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Umarnin na wucin-gadi ya biyo bayan wani korafi da hukumar ta shigar inda ta bukaci a yi hakan. Hukumar ta ce gwamnatin jihar ta tura N666,666,666.64 zuwa asusun bankin don ta samu wata riba.

A wata tattaunawa da kwamishinan labaran jihar Kogi, Kingsley Fanwo yayi da manema labarai a Abuja ya musanta wannan zargin, TheCable ta ruwaito hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"EFCC a bangaren ta, ta rantse a gaban kotu cewa binciken da ta yi ya bayyana mata cewa gwamnatin jihar Kogi ta na da manufa a kan N666,666,666.64 ,” a cewar Fanwo.
“Hukumar ta rantse cewa a ranar 1 ga watan Afirilun 2021 gwamnatin ta kwashi kudi cikin N19,333,333,333.36 suka tura asusun, kudaden da ya kamata su biya ma’aikatansu albashi.

Kwamishinan ya ce, ya kamata a ce EFCC ta na yaki da rashawa amma kuma ta bige da yi wa mutane kage.

Kara karanta wannan

Ba zan cigaba da lamuntar ta'addanci ba, Lalong ga shugabannin Jos

“Abinda ya fi damun mu shi ne yadda ya kamata a ce hukumar EFCC ta na yaki da duk wasu harkokin rashawa na kudi sun kare da zolayar kotu ta hanyar liliyo laifuka da jefa wa wanda bai ji ba bai kuma gani ba.
"Domin gwamnatin Mai girma Gwamna Yahaya Bello ta na daga cikin wadanda suke aiwatar da aikin gaskiya da gaskiya ba tare da almundahana ba,” a cewarsa.

Kano: Gobara ta lamushe rayuka 20, ta lashe kadarorin N5.6m

A wani labari na daban, hukumar kwana-kwanan jihar Kano ta ce an yi asarar rayukan mutane 20 da kuma dukiya mai kimar naira miliyan 5.6 sakamakon gobarar da aka yi a wurare daban-daban a fadin jihar cikin watan Augusta.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’an hukumar ne ya bayar da wannan kiyasin a wata takarda a ranar Laraba a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba

A cewar Abdullahi, hukumar ta samu nasarar ceton rayuka 102 da dukiyoyi da suka kai kimanin naira miliyan 14.7 sakamakon gobara 16 da ta auku a fadin jihar a cikin watan Augustan wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel