Rigingimun PDP ya sa Gwamnonin Jam’iyyar adawa za su yi zama na 3 a cikin makonni 4

Rigingimun PDP ya sa Gwamnonin Jam’iyyar adawa za su yi zama na 3 a cikin makonni 4

  • Gwamnonin PDP a karkashin Aminu Waziri Tambuwal za su yi zama a yau dinnan
  • Darekta Janar na kungiyar gwamnonin PDP, C.I.D. Maduabum ne ya bada sanarwar
  • Za a tattauna yadda za a tafiyar da jam’iyyar, a kuma shirya wa taron NEC a zaman

Abuja - Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP sun sa rana domin su zauna da nufin kawo karshen matsalolin da PDP ta ke ta fuskanta.

The Cable tace wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Darekta-Janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, C.I.D. Maduabum daga garin Abuja.

A jawabin da ya fitar jiya, Maduabum yace gwamnonin adawa za su yi taro a ranar Laraba, 8 ga watan Satumba, 2021, domin shirya wa zaman NEC.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa

A cewar Maduabum, za a tsara yadda za a gudanar da taron majalisar koli ta NEC a zaman da a za ayi yau. A gobe ake sa ran majalisar kolin za ta zauna.

Jaridar tace wannan ne zama na uku da gwamnonin jam’iyyar PDP za su yi domin kawo karshen rigingimun shugabancin da ya barko masu kwanaki.

Gwamnonin Jam’iyyar adawa
Wasu Gwamnonin PDP a taro Hoto: prumetrics.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin da C.I.D. Maduabum ya fitar

“Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Rt Hon. Aminu Waziri Tambuwal, CFR, ya tuntubi abokan aikinsa, ya kira gagarumin taro na musamman.”
“Za ayi taron a (Yau) ranar Laraba, 8 ga watan Satumba, 2021, da karfe 3:00 na rana.”
“Tattaunawar za ta kunshi sha’anin jam’iyya da dabarun daidaita jam’iyyar PDP yayin da za a gudanar da taron NEC a gobe, 9 ga watan Satumba, 2021.”
“Gwamnonin PDP suna kara tabbatar da duk ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da sauran masu ruwa da tsaki game da shirinsu na kifar da gwamnatin APC da ta gaza.”

Kara karanta wannan

2023: Ainihin abin da ya sa APC ke neman tsaida Jonathan yayi mata takarar Shugaban kasa

Vanguard tace gwamnonin sun ce babu abin da APC ta jawo sai karin bakin ciki da wahala a Najeriya, don haka suka yi damar kawar da ita daga kan mulki.

Yajin-aikin ASUU

Rahotanni sun zo mana cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari ta tanka kungiyar ASUU, tayi magana game da yajin-aikin da malamai ke barazanar koma wa.

Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan kwadago, Chris Ngige, ya zargi Malaman Jami’o’in Najeriya da barazana da yajin-aiki domin tada hankalin al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel