‘Yan Taliban suna raba ‘yan mata da maza a Makarantun kasar Afghanistan

‘Yan Taliban suna raba ‘yan mata da maza a Makarantun kasar Afghanistan

  • An yi shamaki tsakanin ‘yan mata da maza a makarantun kasar Afghanistan
  • Yanzu babu dama mace ta hadu da namiji a lokacin da ake daukar darasi a aji
  • Kungiyar Taliban ta fara shigo da wadannan sauye-sauyen bayan karbe mulki

Afghanistan - Mun samu labari cewa ‘yan kungiyar Taliban sun fara kawo canji bayan sun sake karbe mulki a kasar Afghanistan.

BBC Hausa tace yayin da dalibai suka fara rage yawa a makarantun Afghanistan, Taliban tana ta gudanar da wasu sauye-sauye.

Rahoton yace duk da an bar mata da maza su cigaba da halartar aji guda, amma an sa shamaki tsakanin jinsosin ‘yan makarantar.

Akwai shamaki tsakanin mata da maza

An yi amfani da labule an raba bangarorin da nufin a hana mata mu’amala da ‘yanuwansu maza yayin da ake wajen daukar karatu.

Kara karanta wannan

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

A halin yanzu namiji bai isa ya yi mu’amala da takwararsa mace yayin da ake yin darasi a aji ba.

Makarantun kasar Afghanistan
Makarantu a Afghanistan Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: UGC

Bugu da kari, rahoton yace an wajabta wa kowace macen da ta ke karatu amfani da doguwar riga a lokacin da za ta shiga makaranta.

Haka zalika hukumomin Taliban da ke ikirarin aiki da shari’a sun tilasta wa ‘yan mata rufe fuskokinsu, za su rika sa Nikabi.

Tun lokacin da sojojin kungiyar Taliban suka karbe mulki a Afganistan aka fara tsoron cewa za a hana mata zuwa makarantar boko.

An yi dace ba a haramta wa mata zuwa makarantun na boko ba, amma dole su rika amfani da abaya da nikabi idan za su shiga aji.

Mafi yawan malaman musulunci sun tafi a kan cewa addini bai wajabta wa mata rufe fuskoki da tafukan kafa da hannuwansu ba.

Kara karanta wannan

Makiyaya sun daura hotunansu a shafin Facebook din wata mata bayan sun sace mata waya, da dama sun yi martani

Pantami ya zama Farfesa

A Najeriya kuwa an ji labari jami’ar fasaha ta tarayya ta Owerri ta kara wa Dr. Isa Ali Ibrahim matsayi zuwa cikakken Farfesa.

Ministan tarayyar ya samu wannan karin matsayi duk da cewa rabonsa da aji tun a 2016, kuma ba ya koyar wa a wannan jami'ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel