Fastocin Takarar Dakataccen Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Na Kano Sun Bayyana

Fastocin Takarar Dakataccen Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Na Kano Sun Bayyana

  • Fastocin takararar dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa na Kano, Muhuyi Rimingado sun bayyana a birnin Kano
  • Baya ga wasu wurare da aka lika fastocin ne neman takarar gwamna, an gano wasu masu adaidaita sahu sun lika a jikin ababen hawansu
  • Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya dakatar da Muhuyi Rimingado ne saboda kin amsar akanta da aka tura ma'aikatansa

Kano - Fastocin takarar gwamna na dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa da sauraron korafin mutane na jihar Kano, Mallam Muhuyi Rimingado sun bayyana a titunan Kano, The Punch ta ruwaito.

Wasu fastocin da wakilin The Punch ya gano a wurare da dama a birin na Kano suna dauke da rubutu kamar haka "Rimingado for Governor 2023" da aka buga a takarda mai dauke da tamburan jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani tsohon sanata

Fastocin Takarar Dakataccen Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Na Kano Sun Bayyana
Muhuyi Rimingado, Dakataccen Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Na Kano Sun Bayyana.Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Rahoton na The Punch ya ce wasu masu babur mai kafa uku da aka fi sani da adaidaita sahu ko keke Napep suma sun lika hotunan a ababen hawansu.

Abin da yasa aka dakar da Rimingado?

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya dakatar da shugaban hukumar yaki da rashawar ne daga aiki kimanin watanni uku da suka gabata bisa shawarar Majalisar Dokokin Jihar.

Dakatarwa ta biyo bayan kin amincewa da akanta da aka tura masa daga ofishin akanta Janar na Jihar Kano don yin aiki a ma'aikatarsa.

A bangarensa, Rimingado ya ce dokokin da suka kafa hukumar yaki da rashawar ba su bada damar hukumar ta karfi wani ma'aikaci daga ko ina ba sai dai su dauki nasu na kansu.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke dan bautar kasa da ke safarar alawa mai bugarwa daga UK

Jeff Bezos Ya Ɗauka Nauyin Binciken Fasahar Da Za Ta Sa Ɗan Adam Ya Rayu Har Abada

A wani labarin, an samu rahotanni a kan yadda mai kudin duniya, Jeff Bezos ya dauka nauyin fasahar da za ta kara wa rayuwar dan Adam shekaru 50 a kan shekarun da ya debo zai yi a doron duniya.

Kamar yadda LIB suka wallafa, A cewar Bezos wanda daya ne daga cikin biloniyoyin duniyan da suka sanya kudin su a wurin binciken Altos Labs, wata fasahar Silicon Valley ta na aiki a kan hanyoyin kara wa rayuwa tsawo.

Sabon kamfanin ya dauki masana masu tarin yawa daga jami’o’i daban-daban don su yi bincike a kan yadda kwayoyin halittar dan Adam suke tsufa da hanyoyin dakatar dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel