Taliban ta kafa Gwamnati da Ministoci 33, Afghanistan ta tabbata Daular Musulunci
- Mullah Mohammad Hassan Akhund ya zama Firayim Minista a kasar Afghanistan
- Sabon shugaban ya yi aiki a tsohuwar gwamnatin Taliban tsakanin 1996 zuwa 2001
- Kakakin Taliban ya sanar da nadin Ministoci har 33, amma babu wata mace ko daya
Afghanistan - Kungiyar Taliban ta ayyana kasar Afghanistan a matsayin Daular Musulunci, ta kafa gwamnati a karkashin Mohammad Hassan Akhund.
Aljazeera tace Mullah Mohammad Hassan Akhund ne sabon Firayim Ministan kasar. Kafin yanzu ya dade a majalisar Shura, kuma yana cikin manyan Taliban.
A lokacin da Taliban ta yi mulki, Mohammad Hassan Akhund ya rike kujerar Ministan harkokin kasar waje, daga baya ya zama mataimakin Firayim Minista.
An fitar da sunayen Ministoci
Rahoton yace mai magana da bakin Taliban, Zabihullah Mujahid ya fitar da jawabi, ya sanar da nadin mukaman a ranar Talata, 7 ga watan Satumba, 2021.
“Mun san mutanen kasarmu suna ta jira mu kafa sabuwar gwamnati.”
Abdul Ghani Baradar ya zama mataimakin shugaba, yayin da aka nada Sirajuddin Haqqani a matsayin Ministan cikin gida duk da cewa FBI tana neman shi.

Asali: UGC
Sabon Ministan tsaro shi ne Mullah Mohammad Yaqoob. Hedayatullah Badri zai rike Ministan kudi.
Ministan riko na harkokin kasar waje shi ne Amir Khan Muttaqi. Mullah Abdul Ghani Baradar da Mullah Abdul Salam Hanafi sune mataimakan Firayin Ministan.
Jaridar Hindustani Times ta kasar waje, tace a cikin duka wadannan mutane fiye da 30 da aka nada a sabuwar gwamnatin Afghanistan, babu wata mace ko daya.
Amurka tace tana sa ido da kyau a game da abubuwan da suke faru wa a kasar, ganin yadda aka dauko wasu masu kashi a jikinsu, aka ba su mukamai masu tsoka.

Kara karanta wannan
Isa Pantami ya zama Farfesan Jami'a yana rike da kujerar Ministan Gwamnati a Najeriya
Mahaifin Sirajuddin Haqqani shi ne ya kirkiri kungiyar nan ta Haqqani. Shi kan shi sabon Ministan, ana zargin cewa yana da alaka da ‘yan ta’addan Al-Qaeda.
Sauran Ministocin sune:
Mawlawi Noor Mohammad Saqib
Qari Din Hanif
Mawlawi Abdul Hakim Sharie
Mullah Noorullah Noori
Mullah Mohammad Younus Akhundzada
Mullah Abdul Manan Omari
Mullah Mohammad Esa Akhund
Mullah Abdul Latif Mansoor
Mullah Hamidullah Akhundzada
Abdul Baqi Haqqani
Najibullah Haqqani
Khalilurahman Haqqani
Darektocin riko na tsaro, babban banki da gudanarwa:
Abdul Haq Wasiq
Haji Mohammad Idris
Ahmad Jan Ahmady
A makon nan mun samu labari cewa ‘yan kungiyar Taliban sun fara kawo wasu canji musamman a hakar ilmi, bayan sun sake karbe mulkin Afghanistan.
Rahotanni sun ce yayin da dalibai suka fara rage yawa a makarantun kasar Afghanistan, Taliban tana raba mata da maza a aji domin hana mu'amala a jami'o'in kasar.
Asali: Legit.ng