Shugaban kasa ya yi sabon nadi, ya ba Osinbajo sabon aiki, ya nada shugaba a hukumar NCDC

Shugaban kasa ya yi sabon nadi, ya ba Osinbajo sabon aiki, ya nada shugaba a hukumar NCDC

  • Dr. Ifedayo Morayo Adetifa zai hau kujerar Darekta-Janar na hukumar NCDC
  • Sabon Darektan zai canji Dr. Chikwe Ihekweazu wanda zai tafi kungiyar WHO
  • Yemi Osinbajo zai jagoranci kwamitin da zai gyara harkar kiwon lafiya a Jihohi

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Dr. Ifedayo Morayo Adetifa a matsayin sabon Darekta Janar na hukumar NCDC ta kasa.

Jaridar Daily Trust ta wallafa rahoto cewa fadar shugaban kasa ta tabbatar da wannan nadin mukami a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, 2021.

NCDC ce hukumar da ta ke yaki da barkewar cututtuka a Najeriya tun bayan da ta samu cin gashin-kai.

Adetifa Morayo Adetifa zai rike NCDC

Kamar yadda shafin LSHTM ya nuna, Dr. Adetifa Morayo Adetifa ya yi digirinsa na farko a jami’ar Ilorin, jihar Kwara a bangaren ilmin likitanci.

Kara karanta wannan

Isa Pantami ya zama Farfesan Jami'a yana rike da kujerar Ministan Gwamnati a Najeriya

Sabon darektan ya kware a harkar ilmin likitancin kananan yara a asibitin koyar da likitoci na jami’ar UNILAG da ke garin Idi-Araba, jihar Legas.

Adetifa ya yi wani digirin a fannin kula da yadda cututtuka suke yadu wa a al’umma. A wannan fanni ya yi digirin PhD a wata jami’ar Amsterdam.

Shugaban kasa
Shugaban kasa Buhari Hoto: @GarShehu
Source: Facebook

Darektan na NCDC yana aiki ne a makarantar tsabta da ke Landan a kasar Birtaniya, a lokacin da aka ba shi wannan mukami, yana mataimakin Farfesa.

Kafin nan ya yi aiki a kasashen waje, yayi yaki da zazzabin cizon sauro, ya yi bincike a kan tarin tibi.

An ba Osinbajo aiki

Tolu Ogunlesi yace shugaban kasa ya kafa kwamitin da zai gyara sha’ani kiwon lafiya a jihohi da birnin taraya. Yemi Osinbajo ne zai jagoranci kwamitin.

Za a zakulo sauran ‘yan kwamitin ne daga masana da malaman kiwon lafiya. Hadimin shugaban kasar yace za a dauko wakilai daga majalisa da gwamnoni.

Kara karanta wannan

NCC: Babu maganar dawo da Twitter yanzu duk Najeriya tayi asarar Naira Biliyan 200

Ina Chikwe Ihekweazu?

Sabon darektan, Ifedayo Morayo Adetifa zai karbi Chikwe Ihekweazu wanda labari ya zo cewa ya zama matamakin darekta a hukumar lafiya ta Duniya.

A baya an ji shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya aiko wa Dr. Chikwe Ihekweazu takarda yana sanar da shi zai zama sabon shugaban bada agajin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng