Rigimar cikin gidan PDP ya rincabe, kwamiti ya gagara yi wa su Secondus da Wike sulhu

Rigimar cikin gidan PDP ya rincabe, kwamiti ya gagara yi wa su Secondus da Wike sulhu

  • Kwamitin sulhun David Mark ya zauna da Gwamnan Ribas Nyesom Wike
  • David Mark ne aka ba alhakin shawo kan rigimar da ake fama da ita a PDP
  • ‘Yan kwamitin sun rasa yadda za su sasanta Wike da tsohon Shugaban PDP

Port Harcourt - Rigimar da ake fama da ita a PDP ta kara rikida bayan rashin jitu wa da aka samu tsakanin Gwamna Nyesom Wike da Prince Uche Secondus.

Gwamnan jihar Ribas ya ba kwamitin sulhu da Sanata David Mark yake jagoranta sharudan zaman lafiya a PDP, yace dole sai an sauke Uche Secondus.

The Nation tace Nyesom Wike ya kafe a kan bakarsa na cewa dole a canza shugaban jam’iyyar PDP na kasa duk da cewa wa’adinsa zai kare ne a Oktoba.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Jigon jam’iyyar ya ce Ali Modu Sheriff ya cancanci jagorantar jam’iyyar mai mulki

Nyesom Wike ya kuma bukaci Uche Secondus ya janye karar da ya shigar a babban kotun jihar Kebbi da ta bada umarni a sake dawo da shi a kan kujerarsa.

Idan ana so ayi sulhu da gwamna Wike, sai an haramta wa Secondus halartar duk wani taron gudanar wa na NWC, da majalisar koli ta NEC da na BOT.

Rahoton yace amma na-kusa da Secondus ba su gamsu da wannan sharuda da gwamna Wike ya sa ba, suka ce gwamnan ya fifita kan shi ne a yarjejeniyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rigimar cikin gidan PDP ya rincabe, kwamiti ya garara yi wa su Secondus da Wike sulhu
Gwamnonin PDP Hoto: guardian.ng
Asali: Facebook

Secondus yana ganin idan za ayi aiki da doka da tsarin mulkin kasa, babu wani mahuluki a PDP da ya isa tsige shi daga kujerar shugaban jam’iyya na kasa.

Idan har Secondus zai janye karar da ya shigar a kotu, magoya-bayan tsohon shugaban jam’iyyar suna ganin ya zama dole shi ma Wike ya janye karar da ya kai.

Kara karanta wannan

Zulum Ya Ziyarci Faston Da Aka Kashe Ɗansa Yayin Rushe Coci a Borno Don Masa Ta'aziyya

Duk abin da ake yi, Secondus yana ganin yana da sauran kwanaki a ofis, kuma dakatarwar da aka yi masa daga mazabarsa a Ribas ba ta da wani hurumin zama.

Idan aka cigaba da tafiya a haka, aka rasa wanda zai yi hakuri, babu yadda kwamitin na David Mark ya iya illa a nemi yadda za a raba gardamar a gaban kotu.

Dattawan jam’iyyar PDP suna tunanin wannan sabani ya na iya jawo masu matsala a zaben 2023. A ranar Talata ake sa ran kwamitin sulhun zai hadu da Secondus.

APC da Buni suna cikin matsala

Kungiyar SWAGA mai goyon bayan Bola Tinubu a zaben 2023 ta ce dokar kasa ba ta ba Mai Mala Buni damar zama shugaban rikon kwarya a karkashin APC ba.

Lauyoyin SWAGA sun roki Alkali ya fatattaki kwamitin gwamnan jihar Yobe, Mala Buni, sannan a soke matakan da dauka tun da Mala Buni ya shiga ofis a 2019.

Kara karanta wannan

Shugabannin PDP sun zauna da Goodluck Jonathan, sun roke shi ka da ya jefar da Jam’iyya

Asali: Legit.ng

Online view pixel