Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Garkuwa Sun Sace Mutane 18 a Wani Unguwa a Kaduna
- Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari wani unguwa a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna
- Wasu mazauna unguwar sun ce maharan sun kai harin ne misalin karfe 12 na dare sannan sun sace mutum 18
- A halin yanzu babu sanarwa daga rundunar yan sanda game da harin sai dai mazauna unguwar sun ce yan sanda sun isa wurin
Chikun, Jihar Kaduna - A ƙalla mutane 18 ne aka sace cikin adaidaita sahu (Keke Napep) a wani unguwa a ƙaramar hukumar Chikun na jihar Kaduna.
Daily Trust ta ruwaito cewa yan bindiga sun kai hari unguwar misalin ƙarfe 12 na dare.

Asali: Original

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa
Shaidan gani da ido sun ce yan bindigan sun iso da yawa kuma bayan tada hankalin mutane a unguwar, suka yi awon gaba da mutane 18.
Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa har yanzu jami'an yan sanda suna unguwar.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da afkuwar lamarin daga wata majiya na hukuma ba.
Ku saurari ƙarin bayani ...
Asali: Legit.ng