ASUU ta sha alwashin kai DSS kotu a dalilin cin zarafin wani Farfesan Jami’a a hanyar Kano

ASUU ta sha alwashin kai DSS kotu a dalilin cin zarafin wani Farfesan Jami’a a hanyar Kano

  • Malaman jami’a sun yi ca kan hukumar DSS bayan sun taba wani Shugaban ASUU
  • Kungiyar ta ASUU tana zargin jami’an DSS da cin zarafin Abdulkadir Muhammad
  • Wasu rassosin ASUU na barazanar shiga kotu idan ba a biya wa Farfesan hakki ba

Kano - Kungiyar malaman jami’a watau ASUU ta reshen jami’ar Bayero da ke garin Kano, ta yi tir da cin zarafin da jami’an DSS suka yi wa wani malami.

ASUU na zargin DSS da cin zarafin shugabanta na jami’o’in yankin Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad.

Kungiyar ta ASUU take cewa an samu wasu ma’aikatan DSS da suka jibgi Farfesa Abdulkadir Muhammad a lokacin da yake hanyar zuwa taro a Katsina.

Daily Trust a wani rahoto da ta fitar a ranar Talata, 7 ga watan Satumba, 2021, ta ce wannan lamari ya auku da Farfesa Muhammad a cikin watan Agusta.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya yi sabon nadi, ya ba Osinbajo sabon aiki, ya nada shugaba a hukumar NCDC

ASUU - BUK ta yi magana

Rahoton yace ASUU-BUK ta fitar da jawabi ta bakin shugabanta, Farfesa Haruna Musa da sakatarensa na jami’ar tarayyar, Dr. Musa Umar Madugu.

Farfesa Musa da Dr. Madugu sun bukaci hukumar DSS ta binciki lamarin, ta hukunta wanda aka samu da laifi, idan ba haka ba, ASUU za ta kai kara a kotu.

Za a kai DSS kotu
Jami'an DSS a bakin aiki Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Haka zalika shugaban kungiyar ta ASUU ta reshen jami’ar ABU Zaria, Farfesa Rabiu Nasiru, ya kira taron ‘yan jarida a kan wannan lamari a ranar Juma’a.

Wani laifi Farfesan ya yi?

The Abusites ta rahoto Farfesa Nasiru yana cewa DSS sun ci mutuncin Farfesa Mohammed saboda kurum shan gaban wani jami’i a titin zuwa Hadejia.

“Laifinsa idan har akwai bai wuce ya sha gaban wata tawaga da jami’an DSS su ke yi wa rakiya ba.”

Kara karanta wannan

Isa Pantami ya zama Farfesan Jami'a yana rike da kujerar Ministan Gwamnati a Najeriya

“Lamarin ya auku a ranar 18 ga watan Agusta da kimanin karfe 2:00 na rana. Jami’an DSS a wata Hilux ta gwamnatin Kano suka yi wannan aiki.”
“Bayan sun taba shi, sun rusa masa mota, karya madubin gefen motar Mohammed domin nuna isa.”

Shugaban ASUU na ABU Zaria ya nemi ‘yan majalisa su sake yi wa DSS zama, ko a soke sashe na 315 na kudin tsarin mulki saboda burbushin mulkin soja.

Douye Diri ya na ruwan mukamai

Dazu mu ke jin labari cewa Gwamna Douye Diri ya nada mutane 2, 000 a matsayin masu ba shi shawara a jihar Bayelsa, a lokacin da 'Yan PDP suke kuka.

Har yanzu Gwamnan yace bai gama rabon kujeru ba, zai cigaba da bada mukamai, don haka ya yi kira ga masu neman raba kan PDP da su guji yin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel