A shekara daya da rabi, Gwamnan Bayelsa ya nada masu bada shawara kusan 2,000

A shekara daya da rabi, Gwamnan Bayelsa ya nada masu bada shawara kusan 2,000

  • PDP ta shirya taro domin ta karrama Gwamna Diri, Dickson a jihar Bayelsa
  • Jam’iyyar adawar ta karrama Lawrence Ewhrudjakpo da Hon. Fred Agbedi
  • Douye Diri ya maida martani ga masu kukan rabon mukami bai zo kansu ba

Bayelsa - Mai girma gwamnan jiha Bayelsa, Sanata Douye Diri ya bayyana cewa ya ba mutane kusan 2, 000 mukamai dabam-dabam a gwamnatinsa mai-ci.

Jaridar Punch ta rahoto Douye Diri yana wannan bayani a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, 2021.

Douye Diri ya yi wannan bayani a wajen katafaren bikin da aka shirya domin a karrama shi tare da Seriake Dickson, Lawrence Ewhrudjakpo da Fred Agbedi.

Jam’iyyar PDP ta Bayelsa ta yamma ta shirya biki na musamman domin karrama gwamnna, mataimakinsa da tsohon gwamna da ‘dan majalisan Sagbama.

Kara karanta wannan

Rigimar cikin gidan PDP ya rincabe, kwamiti ya gagara yi wa su Secondus da Wike sulhu

Ba a rabon mukamai a Bayelsa?

Da yake bayani, gwamnan ya maida martani ga ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da suke guna-guni a kan cewa gwamnatin Diri da Ewhrudjakpo ba ta ba su mukamai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin watanni 19 da ya yi a mulki, Douye Diri ya bayyana cewa mutane da dama sun amfana da mukaman da ya raba, kuma har gobe ana cigaba da nade-nade.

Gwamnan Bayelsa
Douye Diri da manyan PDP Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ka da a raba kan PDP

“Don Allah ka da ku raba gidan PDP, ka da ku raba mana dangi. Mun tashi daga gwamnatin dawo da kima zuwa gwamnatin cin nasara. Kar ku raba kanmu.”
“Wani lokaci ina damu wa idan mutane suka ce ba na bada mukamai. Lokacin ku zai zo, ku dakata.”
“Mun ba mutane kusan 2, 000 mukamai, kuma har yanzu muna cigaba da raba mukaman. Saboda haka kuyi hakuri, ku jira, lokacinku na zuwa.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa

“Don kurum ba ka samu kujera ba, kana neman raba kanmu, hakan ba zai yi aiki ba. Ka da ku raba mana gida, za mu cigaba da aiki a matsayin bangare guda.”

Rahoton yace gwamna Diri ya yi alkawarin za su cigaba da karbar mutane a tafiyarsu, yace wasu sun shigo, kuma ana lale maraba da zuwansu da hannu biyu.

Jihohi na fama da karancin IGR

Mun ji cewa wasu Gwamnoni 8 ba za su iya rike jihohinsu ba tare da gwamnatin tarayya ba. Daga cikin wadannan jihohi akwai Bayelsa da ba ta tara kudin-shiga.

Alkaluma su na nuna mafi yawan wadannan jihohin duk suna yankin Arewa ne. A daidai wannnan lokaci jihar Legas ta iya tara sama da Naira biliyan 400.

Asali: Legit.ng

Online view pixel