Mutum 5 'yan rakiyar gawar wanda kwalara ta kashe sun mutu a hanyar kai gawa

Mutum 5 'yan rakiyar gawar wanda kwalara ta kashe sun mutu a hanyar kai gawa

  • Wasu mutane biyar sun mutu yayin da suke dawo da dan uwansu gida daga jihar Legas bayan mutuwarsa
  • Wannan ya faru sakamakon kamuwa da cutar kwalara da suka yi, wanda shi ya kashe dan uwan nasu
  • Rahoto ya bayyana cewa, a halin yanzu akwai wasu sauran mutane biyar da ke jinya a asibiti sakamakon cutar

Sokoto - Mutane biyar sun mutu yayin kai gawar dan uwansu da ya mutu sakamakon cutar kwalara a jihar Legas wanda suka dauko don kai shi gida jihar Sokoto.

Wadanda suka mutu an ruwaito cewa 'yan ci rani ne da ke zuwa jihar Legas.

Daily Trust ta ruwatio cewa suna zaune ne a Ojota, yankin da aka ce ya fi fama da cutar kwalara a jihar Legas.

Mutum 5 'yan rakiyar gawar wanda kwalara ta kashe sun mutu a hanyar kai gawa
Cutar kwalara ta hallaka mutane 5 'yan rakiyar gawa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

An bayyana cewa daya daga cikinsu ya kamu da cutar kuma ya mutu jim kadan bayan kamuwarsa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan sanda sun tabbatar da kashe dan uwan Sowore

A cewar majiya:

“Bayan rasuwarsa, sun yanke shawarar kawo gawarsa garinsu, Sanyinna a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto don binne shi.
“Sun dauki motar bas zuwa Sokoto kuma a kan hanyarsu, karin mutane biyar sun kamu da cutar kuma sun mutu kafin isowar su.
”Wasu fasinjoji biyar a halin yanzu suna karbar magani a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko ta Sanyinna.
“An hana motar bas din shiga cikin garin. Mun kira kuma mun sanar da direban cewa ya zarce zuwa wurin da abin ya faru.”

Ardon Sanyinna, Alhaji Shehu Abubakar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce marigayin ya tafi wurin Legas ne neman wurin kiwo mai ciyawa.

An yi jana'izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Cutar kwalara ta barke a Abuja, mutane 604 sun kamu, 54 sun riga mu gidan gaskiya

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kashe Kanin Mai Sahara Reporters, Sowore

Karamar ministar FCT, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, ta ce kananan hukumomi shida a garin sun samu mutane 604 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara inda mutane 54 suka mutu.

Ta fadi haka ne lokacin kaddamar da shirin wayar da kan al'umma game da cutar kwalara da sauran cututtukan da suka barke a yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Ramatu, wacce ta gabatar da bikin kaddamarwar a fadar Agora na Zuba, HRH Mohammed Bello Umar, ranar Asabar, ta nuna damuwa kan karuwar adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar kwalara.

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

A bangare guda, Wani rahoton Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama da Tattalin Arzikin Kasa (SERAP) ya ce ‘yan Najeriya miliyan 27 ne ke samun abin da bai kai Naira 100,000 ba a shekara, inji TheCable.

Kungiyar, a ranar Alhamis 2 ga watan Satumba, ta kaddamar da rahoto mai taken ‘Annobar da aka Manta da Ita: Yadda Cin Hanci da Rashawa a bangaren Lafiya, Ilimi, da Ruwa ke jefa 'yan Najeriya cikin talauci.'

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong

A cewar rahoton, ‘yan Najeriya miliyan 56 na fama da talauci kuma 57.205 daga cikinsu galibinsu na dogaro da kansu ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel