Abin Da Yasa Ba Za a Dena Yin Smogul Ɗin Man Fetur Ba, Shugaban NNPC, Mele Kyari

Abin Da Yasa Ba Za a Dena Yin Smogul Ɗin Man Fetur Ba, Shugaban NNPC, Mele Kyari

  • Kamfanin matatan man fetur ta Nigeria, wato NNPC ta ce zai yi wahala a dena yin fasakwabrin fetur zuwa wasu kasashen
  • Mele Kyari, shugaban NNPC ne ya bayyana hakan yana mai cewa dalili shine akwai banbancin farashi na akalla N100 kan yadda ake sayar da fetur a Nigeria da kasahen da ke makwabtaka da ita
  • Kyari ya ce muddin akwai wannan banbancin farashin yana da matukar wahala a dena yin fasakwabrin duk da cewa suna iya kokarinsu wurin hana wa

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin matatan man fetur na Nigeria, NNPC, ya ce kamfanin da wasu hukumomin tarayya za su cigaba da fama da kallubalen fasakwabrin kayayyakin man fetur saboda babancin farashin man fetur a Nigeria da kasashen da ke makwabtaka da ita, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

The Punch ta ruwaito Shugaban NNPC, Mele Kyari, ne ya sanar da hakan yayin wani jawabi da ya yi wurin taron tattaunawa da kwamitin Majalisar Dattijai na tsara yadda ake kashe kudade ta shirya.

Abin da Yasa Ba Za a Dena Yin Smogul Ɗ in Man Fetur Ba, Shugaban NNPC, Mele Kyari
Shugaban NNPC, Mele Kyari. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

A cewar wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama'a na NNPC, Garba-Deen Muhammad ya fitar, Kyari ya ce akwai banbancin kimanin N100 a farashin kowanne lita daya tsakanin yadda ake sayarwa a Nigeria da kasashen da ke kewaye da ita hakan yasa yana da wuya hana fasakwabri.

Ya ce duk da cewa kamfanin na aiki da hukumomin tsaro domin ganin an yi magananin matsalar, har yanzu akwai sauran aiki duk da cewa ana samun cigaba.

An ambaci Kyari na cewa:

"Idan har akwai banbancin farashi sosai tsakanin yadda ka ke siyarwa da yadda ake samu a wani wuri, tabbas ka sani cewa zai yi wahala a magance matsalar."

Kara karanta wannan

Sanatoci sun jefa CBN, NNPC a matsala, ana zarginsu da sama da fadi duk shekara

Ya jaddada cewa ayyukan masu fasakwabrin yasa yana da wahala a san takamaiman adadin man fetur da ake sha a kasar, yana mai cewa kamfanin kawai za ta iya sanin adadin da aka fitar da tashoshin dakon mai ne amma babu tabbas idan dukkansu ne aka yi amfani da su a kasar.

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya sallami ministoci biyu daga cikin yan fadarsa da ya zaba a ranar 21 ga watan Agustan 2019.

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce bukatar 'sabon jini' ne yasa aka yi sauyin ministocin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An maye gurbin su da Dr Mohammed Mahmood Abubakar, Ministan Muhalali da Abubakar D. Aliyu, Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel