Sanatoci sun jefa CBN, NNPC a matsala, ana zarginsu da sama da fadi duk shekara

Sanatoci sun jefa CBN, NNPC a matsala, ana zarginsu da sama da fadi duk shekara

  • Majalisar Dattawa tace wasu hukumomi na yin sama da fadi da kudin gwamnati
  • Bincike ya nuna akwai hukumomin da ba su maida rarar kudinsu a baitul-mali
  • Tuni irinsu CBN da NNPC suka karyata wannan zargi na Sanata Solomon Adeola

Abuja - A ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, 2021, majalisar dattawan Najeriya ta zargi hukumomi da ma’aikatu da batar da dukiyar gwamnatin tarayya.

Jaridar Punch tace Sanatoci suna zargin wasu hukumomi da kashe kudin shigan da suka tatsa, a maimakon a adana su a cikin asusun gwamnatin kasar.

Shugaban kwamitin tattalin arziki a majalisar dattawa, Sanata Solomon Adeola ya jefi babban bankin kasa na CBN da kuma NNPC da wannan zargi.

Rahoton yace da yake magana a wajen sauraron kudirin tsare-tsaren tattalin arzikin Najeriya na 2022 zuwa 2024, Solomon Adeola ya yi bayanin nan.

Kara karanta wannan

Buhari ya kori ministocinsa: Martani da shawarin 'yan Najeriya ga shugaban kasa

Sanata Adeola ya ware NNPC da CBN

Solomon Adeola mai shekara 52 yake cewa irinsu CBN da NNPC da sauran masu kashe kudi sosai ba su dawo da rarar abin da suka samu a baitul-malin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A wajen kasafin kudi, wasu hukumomin dake tatso kudin-shiga suna kashe duk abin da suka samu da sunan abin da aka ware masu bai ishe su ba.”

Sanatoci
Sanatoci a Majalisa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Daga somin-tabin binciken da kwamitin nan ya yi, abin da muka gano babu dadin ji. Shugabannin wasu hukumomi sun maida hukumomin kayan gidansu.”

Adeola yake cewa hukumomin suna facakar kudi ba tare da an samu wanda zai iya kalubalantarsu ba.

“A cikin hukumomin gwamnati 60, zan iya cewa irinsu NNPC ban san lokacin da suka maida rarar kudinsu zuwa asusun tarayya ba, sai dai kwanan nan da suka ci riba.”

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar kwastam sun cafke wata mota dauke da bindiga da harsasai

Gwamnan CBN, NNPC sun yi martani

Sanatan yace a cikin shekaru biyar zuwa shida, babban bankin CBN bai kawo komai cikin CRF ba.

Mataimakin gwanan CBN, Dr. Kingsley Obiora, ya karyata wannan zargi yace sam ba gaskiya ba ne. Ita ma NNPC tace biyan tallafin mai ne ke cinye kudinta.

A yayin da CBN ta ke cewa tana bin doka, shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa a halin da ake ciki, NNPC ba za ta iya janye tallafin fetur ba.

An ji PDP ta fito tace an saci biliyoyin kudi a NNPC, NHIS, NEMA, NIMASA, da FIRS a mulkin APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng