Gwamnatin Buhari ta na batar da kusan Naira biliyan 2 duk rana a kan tallafin fetur a 2021
- Gwamnatin Tarayya ta kashe N540bn wajen cike rara farashin fetur a watanni 6
- Hakan ya na nufin kullum biyan tallafin mai yana cin Naira biliyan 1.9 a Najeriya
- A dalilin hakan, gwamnati ta samu gibin sama da Naira tiriliyan 1 a asusun FAAC
Abuja – Makudan kudin da ake kashe wa domin biyan tallafin man fetur a Najeriya ya kai Naira biliyan 541 daga watan Fubrairu zuwa Yulin shekarar 2021.
Kamfanin mai na kasa, NNPC ya gabatar wa kwamitin asusun hadaka na FAAC da bayanin abin da ake batar wa duk wata domin mai ya tsaya a farashinsa.
The Nation ta rahoto NNPC yana cewa abin da aka fitar a watanni shida ya haura Naira biliyan 540. Idan aka yi lissafi, kullum ana kashe Naira biliyan 1.93.
NNPC ya bada alkaluman da cewa a watan Fubrairu an kashe N25.37b, sai N60.39b a watan Maris. A watan Afrilu an kashe N61.97b, sai N123.33b a watan Mayu.
A watannin Yuni da Yulin shekarar bana, NNPC ya kashe N126.33b da N103.28b domin ganin farashin lita ya tsaya tsakanin N163 zuwa N165 a gidajen mai.
Gudumuwar NNPC a FAAC ya yi kasa
Jaridar ta rahoto NNPC yana cewa wadannan makudan kudi da ake kashe wa duk wata, sun jawo nakasu sosai wajen abin da ke shiga asusun hadaka na FAAC.
Saboda yadda farashin Dala ya tashi, ‘yan kasuwa sun janye hannunsu daga harkar shigo da man da aka tace, wannan ya sa aka bar NNPC kadai take wannan jigila.
A dalilin haka ne gudumuwar NNPC a asusunn FAAC ya yi kasa sosai a bana. A watan Afrilun 2021, babu abin da kamfanin man ya iya zuba wa a karshen wata.
Ga gudumuwar da NNPC ya bada domin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su raba a cikin watanni shida, an samu gibin akalla Naira tiriliyan 11:
Junairu: N90bn
Fubrairu: N64bn
Maris: N41bn
Afilu: N0bn
Mayu: N38bn
Yuni: N47bn
Yuli: N67bn
Hukumomi suna wuru-wuru - Majalisa
Kwamitin tattali arziki a majalisar dattawa yace babu sisin kobon da mafi yawan hukumomin suke dawowa da shi cikin baitul-mali idan sun samu kudin-shiga.
Sanata Solomon Adeola ya bayyana cewa an yi shekaru akalla biyar CBN bai zuba komai a asusun kasa ba. Ana yi wa kamfanin NNPC irin wannan zargin mai nauyi.
Asali: Legit.ng