Shugaban kwalejin ilimi ya shigar da kwamishana kotu kan kwace masa mata

Shugaban kwalejin ilimi ya shigar da kwamishana kotu kan kwace masa mata

  • Ana fafatawa a kotu tsakanin tsohon kwamishanan noma da Malamin jami'a
  • Matar Malamin ta bukaci kotu ta raba aurensu da mijinta na shekaru 18
  • Malamin yace ya dade yana zargin matarsa na lalata da tsohon kwamishanan

Lafia, Nasarawa - Mataimakin shugaban kwalejin noma, kimiyya da fasaha dake Lafiya, jihar Nasarawa, Peter Aboki, ya shigar da tsohon kwamishanan noman jihar, Alanana Otaki, kan zargin kwace masa matasa.

A cewar kamfanin dillancin labarai NAN, ita kanta matar Peter Aboki, ya shigar kara kotu inda ta bukaci a tsinke igiyar aurenta da mijinta bayan shekaru 18 suna tare.

Yayin zaman kotun da akayi a garin Lafia ranar Litinin, Lauyan Peter Aboki, Shikama Shyeltu, ya bukaci kotun tayi watsi da karar da matarsa ta shigar na raba auren har sai an kammala shari'ar da ya shigar na zinar da yage zargin tana yi da tsohon kwamishana.

Kara karanta wannan

Nasarawa: Malamin makaranta ya maka tsohon kwamishina a kotu kan kwacen mata

A bangaren lauyan matar David Meshi, ya ce matar tace ita kawai ta gaji da auren kuma hakan yasa ta bukaci a raba su.

Shi kuwa tsohon kwamishanan ta bakin lauyansa, Joseph Agbo, ya ce shi dai bai da hannu a lamarin rikicin auren Peter Aboki da matarsa.

Bayan sauraron dukkan bangarorin, Alkalin kotun Abubakar Lanze, ya dage zaman zuwa ranar 15 ga Satumba, 2021 don cigaba da sauraron karar.

Shugaban kwalejin ilimi ya shigar da kwamishana kotu kan kwace masa mata
Shugaban kwalejin ilimi ya shigar da kwamishana kotu kan kwace masa mata Hoto: CourtRoom
Asali: Twitter

Nasarawa Poly ta sallami dalibai 51 kan laifin satar amsa a Jarabawa

A bangare guda, hukumar makarantar fasaha ta jihar Nasarawa watau Naspoly ta fittitiki dalibar 51 kan laifin satar amsa a jarabawar da aka gudanar a kakar karatun 2019/2020.

Mai magana da yawun makarantar, Uba Maina, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba, rahoton NAN.

Kara karanta wannan

Hoton Mutumin Da Kotu Ta Yanke Wa Hukuncin Ɗaurin Gidan Yari Bayan An Kama Shi Yana Satar Doya

Mana yace kwamitin ingancin ilimi na makarantar ta amince da a sallami daliban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng