Barayi sun mayar da kuɗaɗen da suka sata bayan an kai su gaban ƙasurgumin boka

Barayi sun mayar da kuɗaɗen da suka sata bayan an kai su gaban ƙasurgumin boka

  • Wasu barayi a Ghana sun mayar da kudaden da suka sata bayan mai kudin ya je wurin boka don a yi masa aiki a kan su
  • Rahotanni sun bayyana yadda suka saci Ghc10,000 daga wurin mutumin shi kuma ya lashi takobin ganin bayansu
  • Sai da kasurgumin bokan, wanda gidan tsafin sa ya ke wuraren Volta a Ghana ya gayyace su ya tuhume su amma suka musa satar kudin

Ghana - Wasu barayi da suka saci Ghc10,000 daga wurin wani bawan Allah sun lallaba sun mayar da kudin bayan ya kai karar aiki wurin wani kasurgumin boka a gidan tsafin sa na Borkor Bullet Hanson da ke wuraren Volta a Ghana.

Kamar yadda Revival FM suka wallafa a Facebook, da farko bokan ya gayyaci barayin guda 5 zuwa gidansa na tsafi na Borkor Bullet Hanson don su yi bayani, amma suka murje idanunsu suka ce ba su saci kudin ba.

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

Barayi sun mayar da kuɗaɗen da suka sata bayan an kai su gaban ƙasurgumin boka
Barayi sun mayar da kudin da suka sata, suna kuka a gaban boko. Hoto daga Revival FM
Asali: Facebook

Bayan ya kammala tsafin nasa tsaf, daya daga cikin su ya nufi har wurin sa inda ya bayyana cewa tabbas ya saci kudin.

Bayan sa’o’i kadan da isarsu gida daga gidan matsafin, ya koma wurinsa da kudin da ya sata yana rokon shi a kan ya tallafa wa rayuwarsa.

Ya mayar da Ghc 9700 kuma ya bayyana cewa ya kashe Ghc 300.

Zargin cin amana: Saurayi ya zabtare hannun budurwarsa da adda

A wani labari na daban, wani matashi mai suna Chibisi Irem ya datse hannun budurwarsa a ranar Talata a kan zargin ta da soyayya da wani saurayi a Ebonyi.

Punch Metro ta tattaro bayanai akan yadda lamarin ya faru a anguwar Ishieke da ke wata karamar hukuma a Ebonyi ta jihar inda masoyan suke da wurin cin abinci.

Kara karanta wannan

Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo

Bisa wani bincike da Punch Metro ta yi, ta gano cewa Irem ya dade ya na jan kunnen budurwarsa, Chinyere a kan soyayya da wani a anguwarsu sannan ya dade yana raba ta da samari amma ta ki ji.

Chinyere ta cigaba da soyayyarta da wani saurayi har sai da rikicin ya barke tsakaninsu a ranar Talata da safe. Irem ya kai wa budurwar tasa farmaki ne a wurin cin abincinsu suna tsaka da sallamar masu cin abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel