Zargin cin amana: Saurayi ya zabtare hannun budurwarsa da adda

Zargin cin amana: Saurayi ya zabtare hannun budurwarsa da adda

  • A ranar Talata wani Chibisi Irem ya datse hannun budurwarsa bisa zargin ta da soyayya da wani
  • Lamarin ya faru ne a anguwar Ishieke da ke jihar Ebonyi a wurin cin abincin da masoyan suka bude
  • Bayanai sun kammala a kan yadda Chibisi ya yi ta jan kunnen budurwarsa, Chinyere a kan cin amanar sa

Jihar Ebonyi - Wani matashi mai suna Chibisi Irem ya datse hannun budurwarsa a ranar Talata a kan zargin ta da soyayya da wani saurayi a Ebonyi.

Punch Metro ta tattaro bayanai akan yadda lamarin ya faru a anguwar Ishieke da ke wata karamar hukuma a Ebonyi ta jihar inda masoyan suke da wurin cin abinci.

Zargin cin amana: Saurayi ya zabtare hannun budurwarsa da adda
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah. Hoto daga The Punch
Asali: Facebook

Bisa wani bincike da Punch Metro ta yi, ta gano cewa Irem ya dade ya na jan kunnen budurwarsa, Chinyere a kan soyayya da wani a anguwarsu sannan ya dade yana raba ta da samari amma ta ki ji.

Kara karanta wannan

Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo

Chinyere ta cigaba da soyayyarta da wani saurayi har sai da rikicin ya barke tsakaninsu a ranar Talata da safe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Irem ya kai wa budurwar tasa farmaki ne a wurin cin abincinsu suna tsaka da sallamar masu cin abinci.

Hukumar ‘yan sandan jihar Ebonyi sun tabbatar da aukuwar lamarin.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar 'yan sandan, Loveth Odah, ta ce:

Yan sandan jihar sun kama wani saurayi Chibisi Irem, bisa kai wa budurwarsa farmaki da adda a karamar hukumar Isieke da ke jihar Ebonyi.

Lamarin ya faru ne bayan wani rikici ya hada masoyan a wani wurin abinci da suka bude.

Sakamakon farmakin, ya datsi yarinyar a hannunta ta sama da addar. Yanzu haka yarinyar tana asibiti ana kulawa da lafiyarta.

Na ƙosa in ga ka yi nasara, Buhari ya faɗa wa ɗan takarar gwamnan APC a Anambra, Andy Uba

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong

A wani labari na daban, shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ya faɗa wa Sanata Andy Uba, ɗan takarar Jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra cewa ya ƙosa ya ga an zabe shi gwamna, The Cable ta ruwaito.

An shirya gudanar da zaben ne dai a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Buhari, wanda ya yi magana a gidan gwamnati, Abuja yayin tarbar Sanata Uba, ya ce:

"Ina farin cikin maraba da kai a jam'iyyar mu a hukumance. Ina maka fatan alheri. Na ƙosa in ga ka yi nasara, kuma za mu riƙa bibiyar lamarin."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel