Yarbawa Suna Ta Hijira Zuwa Jamhuriyar Benin Saboda Rashin Tsaro a Najeriya, Afenifere

Yarbawa Suna Ta Hijira Zuwa Jamhuriyar Benin Saboda Rashin Tsaro a Najeriya, Afenifere

  • Wani shugaban kungiyar yarabawa, Afenifere ya ce yarabawa suna ta tserewa jamhuriyar Benin da sauran kasashen yamma saboda rashin tsaron Najeriya
  • Ya bayyana hakan ne a wata takardar taron kungiyar da suke yi ko wanne karshen wata wanda suka yi a garin shugaban rikon kwaryar kungiyar, Pa Ayo Adebanjo
  • Afenifere ya bukaci ko wanne dan Najeriya ya kare kan sa daga ‘yan ta’adda sannan ya soki shirin shugaba Buhari na kara bude hanyoyin shanu duk da jama’a ba su so hakan ba

Shugaban kungiyar yarabawa, Afenifere ya ce yarabawa su na ta tsarewa Jamhuriyar Benin da sauran kasashen yamma saboda rashin tsaron Najeriya.

News Wire NGR ta ruwaito yadda ya bayyana hakan a wata takarda wacce kungiyar ta saki a taron ta na karshen ko wanne wata wanda aka yi a garin shugaban rikon kwaryar kungiyar, Pa Ayo Adebanjo.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen Filato: Kungiyar Arewa ta tsakiya ta sha alwashin kare kai daga Makiyaya masu kisa

Yarbawa Suna Ta Hijira Zuwa Jamhuriyar Benin Saboda Rashin Tsaro a Najeriya, Afenifere
Shugaban kungiyar Afenifere, Pa Adebanjo. Hoto: News Wire NGR
Asali: Facebook

A cewar shugaban kungiyar yarabawan, halin da kasar nan take ciki abin duba wa ne.

Afenifere ta ce 'yan Nigeria su kare kansu

Afenifere ya bukaci ‘yan Najeriya su kare kawunan su daga ‘yan ta’adda yayin da yake sukar tsarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kara bude hanyar shanu duk da jama’a suna ta sukar shirin.

News Wire NGR ta ruwaito kamar yadda takardar ta zo; Bayan zurfafa bincike, an gano wadannan matsalolin:

Afenifere ya lura da yadda matsalolin rashin tsaro suka addabi kasar nan har ma da makwabtan ta.

“Wasu daga cikin ‘yan ta’addan suna boyewa da sunan masu hayan babura. Muna kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su tsananta sa ido akan mutanen da suke da alamar tambaya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hallaka dan Sanata Bala Na'Allah da aka yi

“Afenifere ya kula da yadda ta’addanci da laifuka masu kama da hakan har da garkuwa da mutane suka addabai mutanen Yewa, Jihar Ogun, Oke Ogun dake jihar Oyo da sauransu, wanda hakan ya yi sanadiyyar tserewar jama’a jamhuriyar Benin da sauran kasashen yamma. Don haka ya kamata a kawo gyara akan dalilan da suke sanyawa suna yin hakan.
“Afenifere ya lura da yadda ake ta hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a garuruwan yankin yarabawa, musamman ga baki wadanda ba asalin ‘yan yankin bane, hakan yana lalata harkokin neman kudi da noman jama’an yankin har ma da tsaro.
“Afenifere ya bayyana yadda rashin tsaro yake kara yawaita a jihar Kogi, Kwara, Ogun, Oyo, Osun, Ekiti da jihar Ondo. Don haka muke kira ga gwamnati ta samar da kariya ga mazauna yankunan nan.
“Sanin kowa ne cewa Afenifere yana bayan gwamnonin kudu akan dakatar da kiwon shanu a fili.
“Mun amince da salon da gwamnonin kudu maso yamma suka kirkiro na samar da jami’an tsaro kamar Amotekun. Muna basu kwarin guiwar ci gaba da ayyukansu.”

Kara karanta wannan

Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyara Fadar Shehun Borno, Ya Yi Magana Kan Mayakan Boko Haram Dake Mika Wuya

Hotunan doya da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta raba wa manoma a matsayin tallafi ya janyo maganganu

A wani labarin daban, shugaban karamar hukumar Obanliku a jihar Cross Rivers, Evangelist Margaret Inde, ta bawa sabbin manoma tallafin doya da fatanya da adda, daya-daya a matsayin tallafi, rahoton LIB.

SaharaReporters ta ruwaito cewa Inde ta mika kayan tallafin ne yayin bikin cika shekaru 30 da kirkirar karamar hukumar da kuma bikin fitowar sabuwar doya ta bana da aka yi a ranar Juma'a 27 ga watan Agusta.

A wasu hotuna da suka bazu a dandalin sada zumunta, an gano shugaban karamar hukumar tana bawa mutanen yankin ta tallafin doya daya, da fatanya da adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel