2023: Jam’iyyar PDP ta na iya damka wa ‘Dan Arewa tikitin tsaya wa takarar Shugaban kasa

2023: Jam’iyyar PDP ta na iya damka wa ‘Dan Arewa tikitin tsaya wa takarar Shugaban kasa

  • Alamu na nuna cewa PDP za ta iya tsaida ‘dan takarar shugaban kasa daga Arewa
  • Wanda zai zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa zai fito daga Kudancin Najeriya
  • ‘Yan siyasar da za su yi takara a zaben 2023 suna kokarin cusa mutanensu a NWC

Abuja - Akwai yiwuwar cewa jam’iyyar hamayya ta PDP za ta tsaida ‘dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 ne daga Arewacin kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta bayyana wannan ne a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021, ganin cewa ana neman fito da shugaban jam’iyya daga kudu.

A zaman majalisar koli na NEC da PDP ta yi a karshen makon jiya, jam’iyyar ta ce za ta fito da tsarin da za a bi wajen nada sababbin shugabanni.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Wata kotu ta hana Secondus ya ci gaba da zama a matsayin shugaban PDP na kasa

Wata majiya daga jam’iyyar adawar ta shaida wa jaridar cewa majalisar NEC za ta fito da yankunan da za a ba mukamai da takara a zaben 2023.

Ya lissafin 2023 yake?

Akwai jiga-jigan adawa da suke harin kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ta PDP. Mafi yawansu sun fito ne daga jihohin Arewacin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga ciki akwai; Atiku Abubakar; Sule Lamido; Rabiu Kwankwaso; Bukola Saraki; da Aminu Tambuwal.

Masu burin tsaya wa takarar shugabancin Najeriya suna kokarin yadda za su daura mutanensu a majalisar NWC domin suyi nasarar samun tikiti a 2023.

Jam’iyyar PDP a 2019
Jam'iyyar PDP tana kamfe a Kano Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Wanene zai zama shugaban jam’iyya?

‘Yan gaba-gaba a neman kujerar shugaban PDP na kasa sune; Shi kan shi, Prince Uche Secondus; Eyitayo Jegede; Bode George da Prince Ọlagunsoye Oyinlọla.

Akwai kuma irinsu Jimi Agbaje, Eddy Olafeso da Sanata Suleiman Nazif, sai wasu tsofaffin gwamnonin Arewa; Ibrahim Dankwambo da Ahmed Makarfi.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Yan bindiga sun sace Mai takaba kwana 1 da mutuwar Maigidanta a jihar Katsina

Ana ta kishin-kishin cewa Olusegun Obasanjo yana tare ne da Ọlagunsoye Oyinlọla. Shi kuma Atiku Abubakar yana goyon bayan lauyansa, Eyitayo Jegede.

Wani babba a jam’iyyar ya shaida cewa PDP za ta so ne ta tsaida ‘dan Arewa a 2023, sai a fito da mataimakinsa daga Kudu maso gabas ko a kudu maso kudu.

Ra’ayin irinsu Adamu Maina Waziri wanda yana cikin majalisar BOT da Jackson Lekan Ojo shi ne a ba Arewa takara tun da Umaru ‘Yar’adua bai karasa mulki ba.

Arangamar Kwankwaso da Ganduje

A makon da ya wuce ne aka samu labari cewa jirgin sama ya dauko Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje daga Abuja.

Manyan ‘Yan siyasar na Kano sun yi ido biyu, bayan shekara da shekaru suna ta guje wa hadu wa da junansu. Sun shigo jirgi tare, amma sallama kurum ta hadu su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng