Tilastawa kowa yin rigakafin Korona: Wannan ya sabawa hankali, Likitoci sun caccaki gwamnati

Tilastawa kowa yin rigakafin Korona: Wannan ya sabawa hankali, Likitoci sun caccaki gwamnati

  • Gwamnatin tarayya na shawarar wajabtawa kowa yin rigakafin cutar Korona
  • Wannan abu bai yiwa wasu Likitoci da ma'aikatan lafiya dadi ba
  • Mutane da yawa sun riga sun yi nasu rigakafin Astrazeneca

Kungiyar Likitocin Najeriya NMA da kungiyar ma'aikatar kiwon lafiya karkashin gamayyar ma'aikatan asibiti (JOHESU) sun yi martani kan shirin wajabtawa yan Najeriya yin rigakafin Korona.

Yayinda NMA tace mutane na da hakkin cewa ba zasu yi rigakafi ba, sauran ma'aikatan lafiya sun ce wannan shirin tilastawa mutane yi ya saba hankali.

Kakakin gamayyar JOHESU, Mr Olumide Akintayo, a hirar da yayi da jaridar Punch ya yi Alla-wadai da gwamnonin dake kokarin wajabta yiwa mutane allurar.

Yace wannan abu ya sabawa hankali koda ko akwai isasshen kwayoyin rigakafin a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bai kamata a kara farashin kudin wutan lantarki ba'a karawa ma'aikata albashi ba, NLC

A cewarsa:

"Idan ana maganar yin abinda ya kamata, hakan yayi daidai; amma dabbakawa, mun san ba zai yiwu ba. Idan an kawo rigakafi milyan 10 Najeriya tun da cutar Korona ta bayyana, ta yaya zaa tilastawa mutane milyan 200 allura"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Haka kawai ba zaku kafa dokokin da suka saba tunani ba; ba zakuyi magana kawai don dadin yi ba."

Tilastawa kowa yin rigakafin Korona: Wannan ya sabawa hankali, Likitoci sun caccaki gwamnati
Tilastawa kowa yin rigakafin Korona: Wannan ya sabawa hankali, Likitoci sun caccaki gwamnati Hoto: NPHCDA
Asali: Twitter

Shi kuwa Sakatare Janar na kungiyar NMA, Philips Ekpe, yace ba zai yiwu a tilastawa mutane yin rigakafin COVID-19 ba kamar yadda ba za'a tilasta musu zuwa asibiti ba.

Ya ce maimakon haka, kamata yayi a fahimtar da yan Najeriya muhimmancin yin rigakafin.

Gwamnati na shawarar tilastawa kowa yin rigakafin Korona

Jiya mun kawo muku cewa gwamnatin tarayya na shawarar hukunta yan Najeriyan da suka ki yarda a yi musu allurar rigakafin COVID-19.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun kwace Rann, sa'o'i bayan farmakin mayakan ISWAP

Diraktan hukumar kiwon lafiya na kananan asibitoci, NPHCDA, Faisal Shuaib, ya bayyana hakan a hira da manema labarai a Abuja ranar Talata.

Zaku tuna cewa a jihar Edo da Ondo, gwamnatocin tuni sun sanar da hana mutane wadanda basu yi rigakafi shiga wasu wurare ba.

Shuaib yace gwamnati za ta iya amfani da doka wajen hukunta wadanda suka ki yin rigakafi saboda ba zai yiwu a barsu su jefa rayukan wasu cikin hadari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel