Yanzu-yanzu: Gwamnati na shawarar tilastawa kowa yin rigakafin Korona
- Gwamnatin tarayya na gargadin masu cewa ba zasu yi rigakafin Korona ba
- Dr Faisal Shuaib yace lallai gwamnati za tayi shawarar daukan mataki kan wadannan mutane
- A cewarsa kowa na da hakkin cewa ba zai yi rigakafi ba, amma bai da hakkin jefa rayukan wasu cikin hadari
Abuja - Gwamnatin tarayya na shawarar hukunta yan Najeriyan da suka ki yarda a yi musu allurar rigakafin COVID-19.
Diraktan hukumar kiwon lafiya na kananan asibitoci, NPHCDA, Faisal Shuaib, ya bayyana hakan a hira da manema labarai a Abuja ranar Talata, rahoton Punch.
Zaku tuna cewa a jihar Edo da Ondo, gwamnatocin tuni sun sanar da hana mutane wadanda basu yi rigakafi shiga wasu wurare ba.
Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong
Shuaib yace gwamnati za ta iya amfani da doka wajen hukunta wadanda suka ki yin rigakafi saboda ba zai yiwu a barsu su jefa rayukan wasu cikin hadari ba.
Yace:
"Kwamitin lura da lamarin COVID-19 da ma'aikatar lafiya na amfani da damammaki wajen tabbatar da cewa dukkan yan Najeriya sun samu rigakafi."
"Muddin aka samar da rigakafi ga dukkan yan Najeriya, zamu dawo maganar adalci kan wadanda suka yin allurar."
"Idan wasu suka ki yin rigakafin kuma hakan ya zamto hadari ga wasu. toh zamu kafa dokokin kare hakkin sauran jama'a saboda hakkinka bai fi na wasu ba."
"Kana da hakkin cewa ba zaka yi ba, amma ba kada hakkin jefa rayukan wasu cikin hadari."
NAFDAC Ta Amince da Sabbin Rigakafin COVID19, Ta Faɗi Amfani da Hatsarinsu
Hukumar dake kula da ingancin magunguna da abinci, NAFDAC, ta amince da ƙarin rigakafin cutar COVID19 guda biyu da za'a yi amfani da su a Najeriya.
Rigakafin da hukumar ta amince da su sune, Moderna da Sputnik, kuma dukkan sunan amince da su wajen buƙatar gaggawa.
Darakta janar na hukumar NAFDAC, Farfesa Moji Adeyeye, ita ce ta sanar da haka a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Asali: Legit.ng