Bai kamata a kara farashin kudin wutan lantarki ba'a karawa ma'aikata albashi ba, NLC

Bai kamata a kara farashin kudin wutan lantarki ba'a karawa ma'aikata albashi ba, NLC

  • Hukumar NERC ta baiwa kamfanonin raba wuta umurnin kara farashin lantarki daga yau
  • Mataimakin shugaban NLC ya yi Alla-wadai da wannan abu
  • Wannan kari ya biyo bayan karin farashin iskar gas na girki a fadin tarayya

Abuja - Mataimakin shugaban kungiyar kwadagon Najeriya NLC, Joe Ajaero, ya yi kira ga gwamnatin tarayya kada ta sake ta kara farashin kudin wutan lantarki.

Ajaearo ya bayyana hakan yayin hira da yan jarida a shirin Kakaaki na tashar AIT ranar Talata.

Dan kwadagon wanda shina Sakatare Janar na kungiyar ma'aikatan wutan lantarki ya ce ta wani dalili NERC zata kara kudin wuta bayyan ba'a karawa ma'aikata kudin albashi ba.

Ya kara da cewa kamfanonin raba wuta (Discos) na kokarin daurawa talakawa nauyin gazawarsu.

Yace:

"Bara da wannan lamari ya taso, NLC ta sa baki kuma aka kafa kwamitin mutum bakwai karkashin jagorancin karamin ministan kwadago, Festus Keyamo. Ni mamban kwamitin ne."

Kara karanta wannan

Zamu shiga yajin aiki idan aka kara kudin wutan lantarki, NLC

"A lokacin cewa akayi ma ya kamata farashin ya yi sauki idan akayi la'akari da farashin isgar Gas."
Gwamnati a lokacin tace zata tattauna da masu ruwa da tsaki amma har yanzu ba'a aiwatar da komai kan haka ba. Kawai sai kuma yanzu ace za'ayi wani karin kudi yayinda albashin ma'aikata ko motsi bai yi ba."

Bai kamata a kara farashin kudin wutan lantarki ba'a karawa ma'aikata albashi ba, NLC
Bai kamata a kara farashin kudin wutan lantarki ba'a karawa ma'aikata albashi ba, NLC
Asali: UGC

Za'a kara kudin wutan lantarki ranar 1 ga Satumba

Hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya (NERC) ta umurci kamfanonin raba wutar lantarki 11 (Discos) su kara farashin wuta fari daga ranar 1 ga watan Satumba, 2021.

Bisa wani takarda da jaridar TheNation tayi ikirarin gani yau, hukumar NERC ta baiwa kamfanonin damar kara kudin ne a wasikar mai taken "Sanarwan Karin Farashi."

Hakazalika an tattaro cewa a wani takarda mai lamba ”023/EKEDP/GMCLR/0025/2021, kamfanin raba lantarkin Eko (EKEDC), ya sanar da kwastamominsa cewa za'a yi karin kudin wuta daga ranar 1 ga Satumba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel