Hamshakin mai kudi, Aliko Dangote yayi asarar kimanin Bilyan 10 a rana guda

Hamshakin mai kudi, Aliko Dangote yayi asarar kimanin Bilyan 10 a rana guda

  • Arzikin babban attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya sauka da 1.85% ranar Litinin
  • Wannan ya biyo bayan sayar da hannun jarin da wasu masu hannu jari a kamfanin Simintinsa sukayi
  • Har yanzu dai Dangote ne mutum mafi arziki a nahiyar Afrika

Masu hannun jari a kamfanin Simintin Dangote sun yi rashin kudadensu na kimanin N112.46 billion.

Hakazalika arzikin hamshakin mai kudin Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, ya sauko da kashi 1.85% ranar Litinin yayinda darajar kamfaninsa ta sauka.

Arzikin Dangote yanzu dai yana $12.3 billion bayan rashin N95.35 billion ($232 million) a ranar guda.

Tun shekarar 2015, arzikin Dangote na raguwa kadan-kadan.

Kawo yanzu da muke kawo wannan rahoto, Dangote ya sake rashin sama da N24 billion ($60 million), wanda ya rage 0.48% cikin arzikinsa bisa lissafin Forbes.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi luguden wuta, sun kashe ‘Yan bindiga rututu da su ka fake a jejin Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me ya faru da arzikin Dangote?

Binciken Legit.ng ya nuna cewa faduwar da Dangote yayi ya biyo bayan faduwar darajar kamfanin Simintinsa da 2.64% ranar Litinin.

Masu hannun jari a kamfanin sun sayar da hannun jarinsu kan N243/s sabanin N249.6/s da suka saya ranar Juma'ar da ta gabata

Wannan ya haddasa asarar N112.46 billion yayinda arzikin kamfanin ya sauka N4.14 trillion, daga N4.25 trillion da yake ranar Juma'a.

Hamshakin mai kudi, Aliko Dangote yayi asarar kimanin Bilyan 10 a rana guda
Hamshakin mai kudi, Aliko Dangote yayi asarar kimanin Bilyan 10 a rana guda Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Dalilin da ya sa farashin Siminti ya tashi, Kamfanin Dangote

Kamfanin Simintin Dangote ya bayyana farashin da yake sayarwa yan kasuwar Siminti daga masana'antunsa dake Obajana, Gboko, da Ibese.

Dirkatan Kamfanin na shirye-shirye da manyan ayyuka, Devakumar Edwin, ya bayyana hakan a jawabin da ya baiwa manema labarai.

A cewar Devakumar, N2,450 Dangote ke sayarwa yan kasuwar buhun Siminta a Obajana da Gboko, sannan N2,510 a masana'antar Ibese.

Kara karanta wannan

Gwamnatin El-Rufai ta garkame manyan bankuna 4 da ake bi bashin harajin N300.5m

Amma a binciken da Legit.ng Hausa tayi, farashin Siminti a Kaduna da Abuja na tsakanin N3,300 to N3,500.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng