Gwamnatin El-Rufai ta garkame manyan bankuna 4 da ake bi bashin harajin N300.5m
- Hukumar KADIRS mai tattara haraji ta rufe wasu bankuna a jihar Kaduna
- Shugaban KADIRS, Dr. Zaid Abubakar ya bayyana wannan a ranar Litinin
- Abubakar yace ana bin bankunan hudu bashin harajin Naira miliyan 300
Kaduna - Hukumar KADIRS mai alhakin tattara haraji a jihar Kaduna, ta rufe wasu bankuna a dalilin bashin haraji da ake binsu na Naira miliyan 300.5.
The Cable ta ce shugaban Kaduna state Inland Revenue Service, Dr. Zaid Abubakar ya bayyana wannan a lokacin da ya kira taron menama labarai jiya.
Da yake magana a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, 2021, Dr. Abubakar ya bayyana dalilin da ya sa hukumar da yake jagoranta ta dauki wannan matakin.
Ya aka yi bankuna suka tara bashin haraji?
Abubakar yake cewa gwamnatin Kaduna ta na bin bankunan bashin harajin kafa karafunansu da kuma kudin VSAT tun daga shekarar 1999 har zuwa 2020.
Shugaban hukumar ta KADIRS yace akwai wani babban banki da suke bi harajin Naira miliyan 132.6, sannan akwai wanda zai biya Naira miliyan 84.1.
Sauran bankunan biyu za su biya gwamnatin jiha Naira miliyan 60.3 da kuma Naira miliyan 23.5.
Abin da shugaban KADIRS ya fada
Hukumar KADIRS ta dogara da sashe na 104 na dokar haraji wajen daukar wannan mataki. KADIRS ta ce ta sanar da bankunan nauyin da ke wuyansu.
Duk da an rubuta wa bankunan takardu a rubuce, ba su biya wadannan kudi ba. Wannan ya jawo dole ma’aikatan haraji suka je suka rufe sassansu da ke jihar.
“Mun aika takardar neman biyan bukatarmu sau da yawa, kamar yadda doka ta tanada, amma bankunan sun ki zuwa su biya harajinsu ga jiha.”
"Akwai bankin da aka tura wa takarda sa shida, ragowar bankunan sun samu takarda sau hudu. Wannan bai sa sun yiwa kansu karatun ta-natsu ba."
“Babu yadda KADIRS ta iya, dole ta rufe bankunan.”
Zaid Abubakar ya ce bayan an dauki wannan mataki, bankunan sun soma biyan bangaren bashin na su, tare da yi wa gwamnati alkawari za su ciko ragowar.
A watan Yuli ne KADIRS ta garkame rassa hudu na Bankin Fidelity saboda kin biyan sama da Naira miliyan 40 na haraji da gwamnatin Kaduna ke binsa.
Rassan da aka hana aiki sun hada da na titin Ali Akilu, Ahmadu Bello Way, hanyar Polytechnic kan mahadar Maimuna Gwarzo, da kuma na hanyar Kachia.
Asali: Legit.ng