Abin da tsohon Sojan Najeriya ya fada da ya tsokano DIA ta ke neman shi ruwa a jallo

Abin da tsohon Sojan Najeriya ya fada da ya tsokano DIA ta ke neman shi ruwa a jallo

  • Commodore Kunle Olawunmi (mai ritaya) ya yi wata hira da ta tada kura a baya
  • Olawunmi ya fada wa Duniya akwai masu goyon bayan Boko Haram a Gwamnati
  • Kalaman tsohon Jami’in tsaron ya jawo hukumar DIA ta na neman shi a Najeriya

Kunle Olawunmi, wani tsohon jami’in sojan ruwan Najeriya ya yi wasu kalamai a gidan talabijin Channels TV da suka jawo hukumar DIA ta ke nemansa.

Bayan hirar da aka yi da Commodore Kunle Olawunmi mai ritaya, sai aka ji hedikwatar tsaro ta bada sanarwar neman shi, saboda wasu kalamai da ya yi.

The Cable ta tattaro abubuwan da Olawunmi ya fada a hirarsa a kan harin da aka kai a NDA da ta’addancin Boko Haram, da suka yi sanadiyyar neman sa.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU na shirin komawa yajin-aiki kwanan nan, ta ba Gwamnatin Buhari wa’adi

Harin da aka kai a makarantar sojoji

Olawunmi yace ana sakaci wajen yadda ake wangale wa kowa kofar gidan soja domin sallar Juma’a.

“Abin da nake tunani a game da NDA shi ne abin da kowane ‘dan Najeriya yake tunani a yanzu. Abin ya saba hankali, ba za ka kai wa jami’an sojojin NDA hari, ka sha ba.
“Na shafe mako daya a NDA, wani abu ya ba ni mamaki. Duk ranar Juma’a, ana bude wa kowa kofar NDA, ya shigo ya yi sallah a masallaci da zarar karfe 1: 00 ta yi."

Kunle Olawunmi
Kunle Olawunmi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Akwai masu taimaka wa Boko Haram

Tsohon jami’in tsaron ya zargi gwamnatin tarayya da kin hukunta wadanda ake zargi da hannu a rikicin Boko Haram, yace shiyasa sam matsalar ba za ta kare ba

Kara karanta wannan

Yadda aka je har gida, aka maƙure babban ‘Dan Sanata Na Allah inji Gwamnatin Kaduna

“Na fada wa Olonisakin cewa matsalar Boko Haram da ta’addanci a Najeriya shi ne masu daukar nauyin lamarin. Abin ya fi karfinmu, na mu shi ne shirin yaki.”
“Amma ba za mu iya magance matsalar masu mara wa Boko Haram baya da suke cikin gwamnatin Buhari ba, wadanda mu ka sani a wancan lokaci.”
“Kwanan nan an kama mutane 400 da suke ba Boko Haram gudumuwa. Meya sa gwamnati ba ta kai su kotu ba."
“Idan za ku tuna, rikicin Boko Haram ta fara a wajen shekarar 2012 ne, ni ne jami’in da yake kula da bincike a lokacin. Mun kama mutane.”
“Ba zan zo nan in fara kiran sunayen mutanen da yanzu suna gwamnati ba. Wasu sun zama gwamnoni yau, wasu suna majalisa, wasu suna Aso Rock."

Za a musuluntar da Najeriya?

Idan za ku tuna, an ji Olawunmi yana fada wa 'yan jarida cewa za a maida Najeriya kasar Taliban.

Kara karanta wannan

An ayyana neman tsohon jami'in sojan ruwa? DHQ ta yi cikakken bayani

"Idan ka yi lissafi, za ka gane cewa burin shi ne a maida Najeriya kamar wata kasar ‘Yan Taliban."

Ba tare da bada wasu hujjoji ba, tsohon jam’in yace akwai masu shirin musuluntar da kasar nan. Wannan ya jawo 'yan jarida suka kare a hannun hukumar DSS .

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng