Da duminsa: Kotu ta yi fatali da sabuwar bukatar beli da Maina ya mika gaban ta
- Babban kotun birnin tarayya da ke Abuja ta ki sauraron batun neman belin tsohon shugaban PRTT, Abdulrasheed Maina
- Yayin da lauyan Maina ya nemi belinsa, lauyan EFCC, A. M. Ocholi ya ce ya shigar da wata kara wacce ta ci karo da bukatar sa
- Justice Mohammed, alkalin kotun, ya ce ba zai iya sauraron irin wannan bukatar ba a yayin da kotu take hutu har sai ta dawo
FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki sauraron bukatar belin tsohon shugaban PRTT, Abdulrasheed Maina.
Alkalin kotun na hutu, Justice Ahmed Mohammed, ya ki sauraron sabuwar bukatar da lauyan Maina, David Iorhemba ya gabatar gare shi, The Nation ta wallafa.

Asali: UGC

Kara karanta wannan
NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe
Yayin da Iorhemba ya bukaci kotu ta bayar da belin tsohon shugaban PRTT, lauyan EFCC, A. M. Ocholi ya ce ya shigar da karar da ta ci karo da wannan bukatar.
Justice Mohammed ya bayyana cewa, ba shi da hurumin sauraron wannan bukatar yayin da kotu ta ke hutu.
Alkalin ya bukaci a jira har sai Kotu ta dawo daga hutu lokacin da Justice Okon Abang zai dawo tunda dama shi ya fara sauraron shari’ar, sannan idan za su amince ko kuma su yi fatali da wannan bukatar.
Dama ana zargin Maina da wawurar dukiyar da ta zarce naira biliyan daya da sauran laifuka.
Tun ranar 25 ga watan Oktoban 2019 bisa umarnin Justice Abang, Maina yake tsare a gidan gyaran hali da ke Kuje.
Daga baya aka sake shi daga gidan gyaran hali a watan Yuli bayan ya cika duk wasu sharuddan da aka bukata daga wurinsa.
The Nation ta ruwaito cewa, a ranar 18 ga watan Nuwamban 2020 Justice Abang ya kwace belin Maina bayan ya karya wani sharadi na belin.
Bayan nan, an kama shi a jamhuriyar Nijar kuma aka mayar da shi kotu a Disambar da ta gabata inda alkali ya bayar da umarnin a mayar da shi gidan gyaran hali da ke Kuje har sai an kammala shari’ar.
Rayuka 12 sun salwanta a mummunan hatsari da ya auku a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja
A wani labari na daban, mutane 12 sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsari da ya auku a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Hakazalika, wasu mutane 6 sun samu miyagun raunuka duk a cikin mota guda daya a ranar Litinin da rana.
Daily Trust ta ruwaito yadda hatsarin ya auku a daidai Nasarawa Doka a kan titin Kaduna zuwa Abuja a karamar hukumar Kachia da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan
Tattaunawa da Ortom: 'Yan jaridan Channels TV sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS
Asali: Legit.ng