Rayuka 12 sun salwanta a mummunan hatsari da ya auku a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja

Rayuka 12 sun salwanta a mummunan hatsari da ya auku a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja

  • Mutane 12 sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • Sannan akwai wasu mutane 6 da suka samu miyagun raunuka duk a sanadiyyar hatsarin da ya auku ranar Litinin da rana
  • Jami’an tsaro sun ruwaito yadda lamarin ya auku da wata babbar mota kirar Toyota Haice mai dauke da fasinjoji 18

Kaduna - Mutane 12 sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsari da ya auku a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hakazalika, wasu mutane 6 sun samu miyagun raunuka duk a cikin mota guda daya a ranar Litinin da rana.

Daily Trust ta ruwaito yadda hatsarin ya auku a daidai Nasarawa Doka a kan titin Kaduna zuwa Abuja a karamar hukumar Kachia da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin Hausawa 'yan kasuwa da Fulani makiyaya a jihar Delta

Rayuka 12 sun salwanta a mummunan hatsari da ya auku a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja
Rayuka 12 sun salwanta a mummunan hatsari da ya auku a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda jami’an tsaron jihar Kaduna suka ruwaito, hatsarin ya ritsa da wata mota kirar Toyota Hiace ne wacce ta ke dauke da fasinjoji 18 daga Kaduna zuwa Abuja, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Har yanzu ba a gano musabbabin fashewar tayar motar ba.
Fasinjoji goma sha biyu sun rasa rayukansu take yanke. Sannan mutane 6 sun samu miyagun raunuka suna asibiti ana kula wa da lafiyarsu,” a cewar kwamishinan harkokin tsaron cikin gida da na tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan.

Aruwan ya ce gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana alhininsa dangane da faruwar lamarin kuma ya tura sakon ta’aziyyar sa ga iyalan mamatan ya na musu fatan samun rahamar Ubangiji.

Gwamnan ya ce yana yi wa wadanda suka samu raunuka fatan samun sauki cikin gaggawa don su cigaba da harkokin su lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biyu

Rikicin Jos: An tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato

A wani labari na daban, an tsananta tsaro a farfajiyar majalisar jihar Filato a safiyar ranar Litinin. Ponven Wuyep, magatakardan majalisar ya tabbatar da cewa an kara yawan jami'an tsaro amma kuma ana cigaba da aiwatar da sha'anonin mulki.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya musanta rade-radin da ke yawo na cewa an garkame majalisar jihar baki daya.

Asalin jami'an tsaron mu ne a kofar shiga. ma'aikata suna ta shige da fice kuma babu wata matsala, ya sanar da Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel