CJN Tanko ya yi kiran gaggawa ga wasu alkalai 6 kan hukuncin da suka zartar a rikicin PDP

CJN Tanko ya yi kiran gaggawa ga wasu alkalai 6 kan hukuncin da suka zartar a rikicin PDP

  • Shugaban alkalan Najeriya, Justice Tanko Muhammad, ya gayyaci manyan alkalan jihar Rivers, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da Imo don taron gaggawa
  • Wannan ya biyo bayan hukunce-hukunce masu karo da juna da ko wanne alkali cikinsu ya yanke a shari'ar siyasa
  • A makon da ya gabata ne kotu biyu suka yanke hukuci mabanbanta a kan rikicin da ya kunno kai na cikin gida a jam’iyyar PDP

FCT, Abuja - Shugaban alkalan Najeriya (CJN), Justice Tanko Muhammad ya tattaro manyan alkalan jihar River, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da Imo don taron gaggawa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan ya biyo bayan hukuci mabanbanta da ko wannensu ya yanke a jiharsa masu karo da juna.

A makon da ya gabata ne kotu biyu suka yanke hukunce-hukunce masu karo da juna dangane da rikicin da ya barko jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Zulum, Sarakuna, da Shugabannin Borno Sun Fadi Matakin da Zasu Dauka Kan Yan Boko Haram da Suka Mika Wuya

CJN Tanko ya yi kiran gaggawa ga wasu alkalai 6 kan hukuncin da suka zartar a rikicin PDP
CJN Tanko ya yi kiran gaggawa ga wasu alkalai 6 kan hukuncin da suka zartar a rikicin PDP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yayin da babbar kotun jihar Rivers ta dakatar da Uche Secondus daga zama shugaban jam’iyyar na kasa, sai kuma kotun jihar Kotu ta dawo da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan akwai hukunce-hukuncen da suka danganci wasu jam’iyoyin wadanda suka kawo rikici, Daily Trust ta ruwaito hakan.

A takardar gayyatar ta ranar 30 ga watan Augustan 2021 da shugaban alkalan ya aika don gayyatar alkalan, ya na bukatar su bayyana a gaban sa don zaunawa a kan wadannan hukunce-hukuncen.

An janyo hankalina a kan illolin da hukunce-hukuncen da wasu kotu suka yanke wanda ko wanne ya ci karo da wani.
Don haka ya zama tilas a kaina in gayyace ku don mu zauna mu tattauna a kan wannan lamarin. Wannan ya ci karo da yadda NJC ya hana yanke hukunci mabanbanta musamman dangane da matsalolin cikin jam’iyya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Tsohon ministan Afghanistan da ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus

A wani labari na daban, tsohon ministan sadarwa na Afghanistan, Sayed Sadaat ya koma sayar da abinci a kasar Jamus.

Kamar yadda ya bayyana a rahotannin Reuters, Sadaat ya bar kasarsa zuwa Jamus a watan Satumbar da ya gabata bayan kwashe shekaru 2 yana rike da mukaminsa lokacin mulkin shugaban kasa Ashraf Ghani.

Ghani ya bar kasar a ranar 15 ga watan Augustan 2021, bayan Taliban sun amshi mulki, Daily Trust ta ruwaito. Ya tsere ta jirgin sama ya isa Tashkent da ke Uzbekistan daga nan ya wuce Dubai inda suka samar masa da mafaka saboda siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel