Ba zamu yarda ba: Kungiya tayi tsokaci kan karin farashin lantarki da gwamnati tayi
- Wata kungiyar yakin samun ingancin wuta tayi Alla-wadai da kara farashin lantarki
- Hukumar NERC ta bada umurnin kara farashin wuta daga gobe Laraba
- Yan Najeriya da dama sun nuna rashin jin dadinsu kan wannan
Oyo - Gamayyar yakin samun inganci da saukin farashin wutan lantarki watau CARE, shiyyar jihar Oyo, ta yi Alla-wadai da karin farashin wuta da hukumar NERC tayi.
A jawabin da CARE ta saki ranar Talata a Ibadan, kungiyar ta yi watsi da wannan kari da hukumar NERC tayi, rahoton DN.
Tace:
"CARE tayi Allah-wadai da umurnin kara farashin wutan lantarki da hukumar NERC tayi."
"Kara farashin wuta a irin wannan lokaci da yan Najeriya ke fama da kuncin tattalin arziki sakamakon COVID-19 da kuma matsin tattalin arziki rashin tausayi ne."
"CARE na da ra'ayin cewa babu wani dalilin kara farashin wuta tunda karin da akayi a baya bai tsinana wani ingancin samun wuta ba."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Maimakon haka, yawancin mutane na fama da karancin wutan lantarki sannan kuma ana tilastasu biyan kudi."
Za'a kara kudin wutan lantarki ranar 1 ga Satumba
Kun ji cewa hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya (NERC) ta umurci kamfanonin raba wutar lantarki 11 (Discos) su kara farashin wuta fari daga ranar 1 ga watan Satumba, 2021.
Bisa wani takarda da jaridar TheNation tayi ikirarin gani yau, hukumar NERC ta baiwa kamfanonin damar kara kudin ne a wasikar mai taken "Sanarwan Karin Farashi."
Hakazalika an tattaro cewa a wani takarda mai lamba ”023/EKEDP/GMCLR/0025/2021, kamfanin raba lantarkin Eko (EKEDC), ya sanar da kwastamominsa cewa za'a yi karin kudin wuta daga ranar 1 ga Satumba, 2021.
Asali: Legit.ng