Da dumi-dumi: Za'a kara kudin wutan lantarki ranar 1 ga Satumba

Da dumi-dumi: Za'a kara kudin wutan lantarki ranar 1 ga Satumba

  • Gwamnatin tarayya ta amince da kara farashin wutar lantarki daga Satumba
  • Wannan ya biyo karin da akayi a 2020 ta ninki biyu
  • Tuni wasu kamfanonin raba wuta sun fara sanar da kwastamominsu

Lagos - Hukumar lura da wutar lantarkin Najeriya (NERC) ta umurci kamfanonin raba wutar lantarki 11 (Discos) su kara farashin wuta fari daga ranar 1 ga watan Satumba, 2021.

Bisa wani takarda da jaridar TheNation tayi ikirarin gani yau, hukumar NERC ta baiwa kamfanonin damar kara kudin ne a wasikar mai taken "Sanarwan Karin Farashi."

Hakazalika an tattaro cewa a wani takarda mai lamba ”023/EKEDP/GMCLR/0025/2021, kamfanin raba lantarkin Eko (EKEDC), ya sanar da kwastamominsa cewa za'a yi karin kudin wuta daga ranar 1 ga Satumba, 2021.

Eko Disco ya sanar da kwastamominsa cewa:

"wannan kari zai bayyana a kan takardar biyan kudin wuta na Oktoba 2021, wanda ke nuna adadin wutan da akayi amfani da shi a watan Satumba."

Kara karanta wannan

Har yaran masu kudi muna kamawa, Shugaban hukumar Hisbah

"Amma kwastamomi masu amfani da mita, muna kira gareku ku gyara mitocin zuwa sabon farashin da NERC tayi umurni."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayinda aka tuntubi mai magana da yawun hukumar NERC, bai daga wayarsa ba kuma bai amsa tambayar da akayi masa ta sakon akwatin SMS ba.

Da dumi-dumi: Za'a kara kudin wutan lantarki ranar 1 ga Satumba
Da dumi-dumi: Za'a kara kudin wutan lantarki ranar 1 ga Satumba
Asali: Twitter

Ya kamata a kara farashin wutan lantarki a Najeriya, yayi arha da yawa

Zaku tuna cewa bankin duniya ta ce harajin da aka daura ma 'yan Najeriya ba ya nuni da irin kudin da kamfanin samar da lantarki da kuma kamfanin da take rarraba wutan.

An bayyana hakan ne a cikin rahoton 'Bangaren sake fasali' wanda Bankin Duniya ya fitar a ranar Talata, cewa an kashe sama da tiriliyan N1.68 a kan karin mafi karanci kudin harajin wuta daga shekaran 2015 zuwa 2019 wanda Shugaban kasa yayi.

Kara karanta wannan

An saki Matar da ta kashe mijinta a Kano bayan shekaru 7 a Kurkuku

Babban Bankin Duniya ya ce kashi 40% na masu hannu da shuni a Najeriya su ke cin kashi 80% na kudin haraji da ake kashewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel