Da duminsa: Tsohon Sojan da gwamnati ta alanta nema ruwa a jallo ya dira ofishin DIA
- Tsohon Sojan da ake nema ruwa a jallo don hirar da yayi kan Buhari da Boko Haram ya isa ofishin DIA
- Sojan mai ritaya yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram
- A cewarsa, akwai gwamnoni da Sanatoci cikin binciken da aka gudanar
Abuja - Tsohon Sojan Najeriya, Commodore Kunle Olawunmi (mai ritaya), ya dira ofishin hukumar leken asirin Soji (DIA) dake Abuja bayan gwamnati ta alanta nemansa ruwa a jallo.
Hotuna da SaharaReporters sun nuna lokacin da tsohon Sojan ya dira ofishin DIA tare da lauyoyinsa ranar Talata.
Gwamnati ta alanta nemansa ne kan hirar da yayi a ChannelsTV inda yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram kuma an alanta neman tsohon sojan da yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram cikinsu akwai gwamnoni da Sanatoci.
Majiyar tace:
“Navy Commodore Kunle Olawunmi ya dira ofishin DIA a Abuja. Yana tare da lauyoyinsa."
"Da farko sun alanta nemansa ruwa a jallo amma da jama'a suka samu labarin haka sai suka ce gayyatarsa suka yi."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga cikin lauyoyinsa dake wajen akwai shahrarren Lauya, Femi Falana da kuma Abubakar Marshall.
An alanta neman tsohon sojan da yace gwamnati ta san masu daukar nauyin Boko Haram
Gwamnatin tarayya ta alanta neman tsohon Sojan ruwa, Commodore Kunle Olawunmi, ruwa a jallo kan hirar da yayi kan shirin 'Sunrise Daily' na tashar ChannelsTV.
Kunle Olawunmi, wanda yanzu Farfesa na kan lamuran tsaro ya gabatar da hirar ne ranar Laraba, 25 ga Agsuta, 2021.
Wace hira yayi da yan jaridan ?
Tsohon Sojan Ruwa, Commodore Kunle Olawunmi, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta san wadanda ke daukan nauyin yan ta'addan Boko Haram da suka addabi kasar.
Ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida a shirin Sunrise Daily na ChannelsTV.
Olawunmi yace:
"Su (gwamnati) sun sani. A Afrilun shekarar nan, gwamnati ta ce ta damke yan kasuwar canji 400 dake daukan nauyin yan Boko Haram. Haka suka fada mana."
"Mun san su fa, me zai hana wannan gwamnatin, idan ba siyasa take ba, ta fito da wadannan mutane su gurfana a kotu."
Ya ce gwamnatin tarayya na jan kafa wajen yaki da ta'addanci saboda wasu daga cikin masu daukar nauyin Boko Haram na cikin gwamnatin.
Asali: Legit.ng