Gwamnati fa ta san masu daukan nauyin yan Boko Haram, wasu gwamnoni ne yanzu: Tsohon Jami'in Soja

Gwamnati fa ta san masu daukan nauyin yan Boko Haram, wasu gwamnoni ne yanzu: Tsohon Jami'in Soja

  • Wani tsohon soja ya ce akwai gwamnoni da Sanatoci cikin wadanda ke goyon bayan Boko Haram
  • Tsohon Sojan ya ce har yanzu gwamnati bata gurfanar da yan kasuwan canjin da aka kama kwanaki ba

Lagos - Tsohon Sojan Ruwa, Commodore Kunle Olawunmi, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta san wadanda ke daukan nauyin yan ta'addan Boko Haram da suka addabi kasar.

Ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida a shirin Sunrise Daily na ChannelsTV.

Olawunmi yace:

"Su (gwamnati) sun sani. A Afrilun shekarar nan, gwamnati ta ce ta damke yan kasuwar canji 400 dake daukan nauyin yan Boko Haram. Haka suka fada mana."

Za ku tuna cewa a watanni baya, faar shugaban kasa ta yi alkawarin cewa zata wallafa sunayen wadanda ke daukan nauyin yan Boko Haram.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Na Tsallake Harin Yan Boko Haram Sama da 50, Gwamna Zulum

Amma har yanzu, fadar shugaban kasa bata cika wannan alkawarin ba, kuma tsohon Sojan yace wannan bai dace ba.

Ya kara da cewa:

"Mun san su fa, me zai hana wannan gwamnatin, idan ba siyasa take ba, ta fito da wadannan mutane su gurfana a kotu."

Ya ce gwamnatin tarayya na jan kafa wajen yaki da ta'addanci saboda wasu daga cikin masu daukar nauyin Boko Haram na cikin gwamnatin.

Gwamnati fa ta san masu daukan nauyin yan Boko Haram, wasu gwamnoni ne yanzu
Gwamnati fa ta san masu daukan nauyin yan Boko Haram, wasu gwamnoni ne yanzu: Tsohon Jami'in Soja Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

Commodore Olawunmi ya ce lokacin da yake mamban kwamitin leken asiri, sun damke wasu yan ta'adda kuma sun fada musu sunayen wasu dake daukan nauyinsu.

Yace:

"Ba zan zo nan in ambaci sunayen mutanen wadannan yara da muka kama suka fada mana ba saboda suna cikin gwamnatin nan."
"Wasu daga cikinsu gwamnoni ne yanzu. Wasu na majalisar dattawa. Wasu daga cikinsu na Aso Rock."

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Ba dukkan tubabbun 'yan Boko Haram bane 'yan ta'adda, Gwamna Zulum

Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ce ba duk tubabbun mayakan Boko Haram da suka tuba cikin kwanakin nan ne ‘yan ta’adda ba.

The Cable ta ruwaito cewa, Gwamnan ya ce fiye da ‘yan ta'adda 2600 ne suka yada makamansu, kuma da yawansu sun yi tuba ta hakika

Zulum ya yi wannan bayanin ne yayin tattaunawa da manema labarai bayan wani taro da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng