Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Bada Tallafin Sama da Miliyan N4m a Gina Coci, Mutane Sun Magantu

Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Bada Tallafin Sama da Miliyan N4m a Gina Coci, Mutane Sun Magantu

  • Babban limamin Ghana ya tallafawa kiristoci da dala dubu 10 su gina babbar coci a ƙasar
  • Lamarin ya bar baya da ƙura, inda al'ummar musulmam kasar suka nuna fushinsu bisa wannan tallafin
  • Sai dai mai magana da yawun malamin yace sam babu kurkure a kan baiwa kiristoci tallafin gina Coci

Ghana - Babban limamin ƙasar Ghana, Dr Osman Nuhu Sharubutu, ya baiwa kiristoci tallafin dala dubu 10 kwatankwacin sama da miliyan N4m domin gina babbar coci.

Sai dai lamarin ya jawo kace-nace tsakanin al'ummar musulmi a kasar, inda suka nuna rashin jin dadinsu bisa matakin da limamin ya ɗauka.

A cewar wasu daga cikin musulman Ghana sam bai kamata Malam Sharubutu ya mika waɗannan zunzurutun kuɗin ga kiristoci ba domin akwai yankunan da ake bukatar gina masallaci.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

BBC Hausa ta ruwaito wata mata musulma na cewa kiristoci ba su taimakon musulmai wajen gina masallaci sai daga wata ƙasar ake zuwa a tallafa.

Babban Malamin Ghana, Dr Osman Nuhu Sharubutu
Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Bada Tallafin Sama da Miliyan N4m a Gina Coci, Mutane Sun Magantu Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Matar tace:

"A baya musulmai sun nemi gudummuwa domin gina masallaci da zasu rinka Ibada, muna tare da kirintocin nan basu tallafa mana ba. Sai daga ƙasar Turkey aka zo aka gina mana."

Meyasa babban Limami, Malam Sharubutu, ya yi haka?

A ɗaya ɓangaren kuma, kakakin babban limamin, Sheikh Armaya'u Shu'aibu, ya yi karin haske da cewa uban gidansa ya yi hakane domin inganta alakar musulmi da kiristoci a ƙasar.

A cewar Sheikh Shu'aibu, kiristoci ne suka kai masa ziyarsa sannan suka gabatar masa da kudirinsu na kokarin gina wurin ibadarsu.

Yace:

"Masu jagorantar gina cocin ne suka kaiwa malam ziyara ta musamman tare da sanar da shi kudirinsu, shi kuma ya ga bara ya ba da tallafi daga ɓangarensa saboda ana tare."

Kara karanta wannan

Hotunan Gidan da Aka Tsinci Gawar Babban Ɗan Sanatan APC a Kaduna

Shin malamin yana tallafawa musulmai?

Bugu da kari, sheikh Shu'aibu ya bayyana cewa malamin na iya kokarinsa wajen tallafawa musulmai amma ba zai iya dauke musu komai ba.

Ya kara da cewa daga cikin irin kokarin da yake wa musulmai, malamin yana biyan kuɗin magani ga waɗanda suka samu jarabtar jinya a asibiti.

Hakazaliƙa yace yana tallafawa ɗalibai sosai da kuɗin da zasu zurfafa ilimin su a ɓangarori da dama, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta gano cewa a kasar Ghana akwai musulmai kusan kashi 13%, inda suka fi rinjaye a arewacin ƙasar.

A wani labarin kuma Sanata Ahmad Lawan Ya Kai Ziyara Fadar Shehun Borno, Inda Ya Yi Tdokani Kan Mayakan Boko Haram Dake Mika Wuya

Shugaban sanatoci, Sanata Ahmad Lawan, ya kai ziyara fadar mai martaba shehun Borno domin masa ta'aziyya.

Lawan yace mika wuyan mayakan Boko Haram wata hanya ce mai kyau ta kawo karshen matsalar tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Idan Bamu Yi Dagaske Ba Wataran Abujan da Muke Takama Ba Zata Zaunu Ba, Ministan Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel