Naira ta yi rugu-rugun da ba ta taba yi ba a tarihi, Darajar Dala 1 ta kai N527

Naira ta yi rugu-rugun da ba ta taba yi ba a tarihi, Darajar Dala 1 ta kai N527

  • An saida Dala a kan N527 a makon nan, abin da ba a taba yi ba
  • Darajar Naira ya na kara yin kasa, Dala tana kara tsada a kasuwa
  • Ana ta fama da karancin Dalar tun da aka daina ba ‘yan canji kudi

Nigeria - Darajar Naira ta cigaba da yin kasa a kasuwar canji a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, 2021. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.

Rahoton ya bayyana cewa Naira ta kara rasa kima a kan Dalar Amurka, inda kudin Najeriyar ya yi mummunan faduwar da bai taba yin irinsa ba.

Nawa ake saida $1 a yau?

A farkon makon ne farashin Dalar Amurka $1 ya kai N527 a kasuwar canjin kudin kasashen waje. Abin da ba a taba gani a tarihin tattalin arziki ba.

Jaridar ta ce a cikin ‘yan makonnin nan, Naira ta na ta yin kasa yayin da Dala ta ke kara daraja daga N522 zuwa N524 a karshen makon da ya gabata.

Sai dai kuma sabanin haka, a kasuwar masu shigo da fita da kaya a Najeriya, Naira ta kara kima a jiya. FMDQ ta ce darajar Dala ta ragu a makon nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An saida Dalar Amurka a kan N411.63 a jiya, akasin N412 da aka rika saida ta a karshen makon jiya.

Gwamnan CBN
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Hoto: www.cbn.gov.ng
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta tabbatar da wannan rahoto, inda tace Dala ta yi tsadar da ba ta taba yi ba.

Alkaluman da aka samu daga kafar abokiFX.com mai tattara farashin kudin waje a Legas ya nuna cewa Naira ta na yin sululu a halin da ake ciki.

Menene ya jawo tashin Dala?

Shaibu Isah wani ‘dan kasuwar canji a Akwa Ibom, ya zargi matakin da gwamnan CBN ya dauka a matsayin abin da ya jawo Dala ta ke ta doke Naira.

“Babban bankin kasa na CBN suke jawo farashin Dalar Amurka ya tashi a kan Naira. A halin yanzu,muna ta kokarin neman Dala ne ta ko ina.”
“Babu wanda ke kula da kasuwar canji, kowa zai nemo Dalarsa ne, ya saida a yadda ya ga dama.”

Babu ruwan CBN da BDC

A karshen watan Yuli ne babban banki na CBN ya bada sanarwar an daina saida Dala ga ‘yan canji, hakan ya kara jawo karancin Dala a kasuwa.

Tun a kwanakin baya aka ji cewa dakatar da saida Dala ga 'yan kasuwar canji ya bar baya da kura, inda farashin Naira ke cigaba da fadi war-was.

Asali: Legit.ng

Online view pixel