An kafa tarihi: Buhari ya sanar cewa NNPC ta samu ribar N287bn a 2020, karon farko a shekaru 44

An kafa tarihi: Buhari ya sanar cewa NNPC ta samu ribar N287bn a 2020, karon farko a shekaru 44

  • NNPC ta bayyana ribar naira biliyan 287 da ta samu a karshen shekarar 2020, a karo na farko cikin shekaru 44 a tarihin kamfanin
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ministan fetur ya sanar da hakan ne a wata takarda ta ranar Alhamis
  • Buhari ya bayyana yadda asarar kamfanin ta rage daga naira biliyan 803 zuwa naira biliyan 1.7 daga shekarar 2019 zuwa 2020

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa tarihin da ba a taba kafa wa ba a tsawon shekaru 44 a tarihin kamfanin man futur din.

Shugaba Buhari ya bayyana yadda NNPC ta samu ribar naira biliyan 287 a karshen bisa kididdigar 2019 zuwa shekarar 2020, The Cable ta ruwaito.

Shugaban kasan wanda shine kuma ministan man fetur ya bayyana wadannan tarin nasarorin a wata takarda ta ranar Alhamis, 26 ga watan Augustan 2021.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Tattalin arzikin Najeriya ya karu da 5.01% a cikin wata 3 kacal

A karon farko, Buhari ya sanar da cewa NNPC ta samu ribar N287bn a shekarar 2020
Kamfanin Matatan Mai Na Nigeria, NNPC. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya sanar da yadda asarar NNPC ta ragu daga naira biliyan 803 daga shekarar 2018 zuwa naira biliyan 1.7 a shekarar 2019 sannan daga karshe ya bayyana ribar da aka samu gaba daya a 2020.

A cewar Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, a wata takarda ta ranar Alhamis kamar yadda ya yanko jawabin shugaban kasa:

“Ina farin cikin sanar da kacokan ribar da aka samu bayan cire haraji na shekarar 2020 da NNPC ta samu ta naira biliyan 287. An samu wannan bayanin ne bayan kididdigar duk shekara da aka kammala,”

An samu wannan nasarar ne sakamakon dagiya da zage damtsen shugaban kasa don mutanen Najeriya su amfana da romon da aka samu ta ma’adanan kasa.

“Na bai wa NNPC umarnin dinga sanar da duk wasu bayanai na kididdigar kudade kamar yadda doka ta tanadar don ko wanne dan Najeriya ya san halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Kungiyar kare hakkin jama'a ta kai karar Buhari a kotu kan ‘bacewar’ Naira Biliyan 106 a 2018

“Ina taya ma’aikata da shugabannin kamfanin murnar samun wadannan nasarorin sannan muna fatan ci gaba da ganin irin haka a shekaru masu zuwa.”

Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Edo ta ce za ta saka tsauraran matakai a bankuna, majami'u, masallatai da wuraren shagulgulan biki kan duk wanda bai nuna shaidar yin riga-kafin cutar korona ba daga watan Satumba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamna Godwin Obaseki na jihar ya sanar da hakan ranar Litinin yayin kaddamar da kashi biyu na riga-kafin cutar korona a Benin City.

Ya ce cutar korona nau'in Delta na yaduwa sosai kuma tana cigaba da yaduwa a kowanne lokaci, lamarin da yasa dole jama'a su yi riga-kafin cutar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel